Sakamakon zaɓen Ukraine | Siyasa | DW | 08.02.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon zaɓen Ukraine

Jagoran ´yan adawar ƙasar Ukraine Viktor Yanukovich ya yi iƙirarin lashe zaɓen shugaban ƙasar da wani rinjaye da bai taka kara ya karba ba

default

Allunan kamfen: Yanukovich da Tymoshenko

To sai dai abokiyar hamaiya kuma Firaministar ƙasar a yanzu Yulia Tymoshenko ta ƙi rungumar ƙaddara tana mai cewa za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu ko kuma ta kira magoya bayanta su gudanar da zanga-zanga idan aka tabbatar da maguɗin zaɓe.

Bayan an kammala ƙidayar kimanin kashi 95 cikin 100 na ƙuri´u da aka kaɗa, wani jami´in hukumar zaɓen ƙasar ya faɗawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa jagoran adawa Viktor Yanukovich mai ra´ayin ƙasar Rasha zai kasance wanda yayi nasara kuma tazarar tsakaninshi da Yulia Tymoshenko mai goyon bayan ƙasashen yamma, za ta ƙaru. Domin yanzu haka ana ci-gaba da tattara sauran sakamako daga yankunan da yake da ƙarfi wato na kudanci da kuma gabashin ƙasar. To sai dai magoya bayan Tymoshenko, wadda ke riƙe da mukamin firaminisa a yanzu sun ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare suna masu nuni da cewa dole ne a jira har  sai an kammala ƙidayar ƙuri´un. Ita ma kanta ba ta yanke ƙyaunar cewa sakamakon na iya canzawa ba.

"Ina taya kowa murnar bikin ɗorewar demokuraɗiyya inda ake bawa kowa damar bayyana ra´ayinsa don bawa wannan ƙasa ta mu kyakkyawar makoma. Ina goyon bayan samun sabuwar ƙasa ta Ukraine, wadatacciya a tsakanin ƙasashen Turai."

Tymoshenko ta yi tuni da maguɗin zaɓen da Yanukovich ya tabƙa a shekara ta 2004, wanda ta ƙalubalanci sakamakonsa ta hanyar shirya zanga-zangar gama gari.

To sai dai a nasa ɓangaren Viktor Yanukovich ya ce ko tantama babu a wannan karon shi ya lashe zaɓe. Ya na mai cewa ba wanda ya isa ya hana shi wannan nasara.

"Wannan zaɓen yana matsayin matakin farko da muka yi na samarwa ƙasar mu kyakkyawar makoma. Wannan muhimmin abu ne a garemu yanzu da ma gaba. Hakan zai ba mu damar haɗa kai tare domin tinkarar matsalolin Ukraine."

Sakamakon da aka samu yanzu ya bawa Yanukovich rinjayen kashi 2.09 cikin 100 akan firaminista Tymoshenko. Bisa haka ne ma manazarta al´amuran yau da kullum suka ce Tymoshenko wadda tun da farko ta gargaɗi Yanukovich da ka da yayi riga malam masallaci wajen ayyana kansa a matsayin wanda yayi nasara, za ta samu ƙarfin guiwar ci-gaba da ƙalubalantar sakamakon zaɓen.

Duk wata nasara da Yanukovich zai samu ka iya karkata wannan ƙasa mai yawan al´uma miliyan 46 zuwa ga Rasha, bayan an shafe shekaru biyar na rikicin siyasa da taɓarɓarewar tattalin arziki da ya sa murna ta koma ciki bayan ɗokin da aka yi na samun wani ci-gaba mai ma´ana bayan zanga-zangar nan ta Orange Revolution a shekara ta 2004.

Dukkan ´yan takarar biyu sun yi alƙawarin haɗewa da sauran ƙasashen Turai da inganta hulɗoɗi da Mosko, to amma Tymoshenko ta fi karkata ga ƙasashen yamma. Sannan ba a tsammanin Yanukovich zai ƙarfafa neman shiga ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO.

Ko yaya zata kaya dai, za a ci-gaba da samun rarrabuwar kawuna tsakanin yankunan gabashi da kudanci dake goyon bayan Rasha da al´umar tsakiya da yammacin ƙasar masu ɗasawa da ƙasashen yamma.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadisou Madobi