Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a tsibirin Comores | Labarai | DW | 16.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a tsibirin Comores

Hukumar zaɓe a tsibirin Comores, ta bayyana Ahmed Abdullah Mohamed Sambi, a matsayin ɗan takara da lashe zaɓen shugaban ƙasa, na ranar lahadi da ta wuce.

Sambi, da magoya bayan sa ke kira, Ayatolah, ya samu kussan kashi 59 daga cikin 100, na yawan ƙuri´un da aka kaɗa, inji ministan kulla da harakokin zaɓe ,Ali Abdallah.

A yayin da yi taron manema labarai, a Monroni baban birnin tsibirin, saban shugaban, ya bayyana wannan nasara ,da bukatar cenji, da al´ummar Comores ke da ita, a kan harakokin mulki.

Masu adawa da Mohamed Sambi, na tunin cewar, zai ƙadamar da shari´ar musulinci a wannan ƙasa.

Ibrahim Halidi ɗan takara da ya zo sahu na 2, ya ta shi da jimmilar kashi 28 bisa 100, duk da goyan bayan da ya samu, daga shugaban ƙasa mai barin gado, Azaly Assumani.

Sai kuma dan takara na 3, Mohamed Jafari, da ya samu kashi kussan 14 bisa 100, na jimmilar ƙuri´un da ka jefa.