1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon Zaɓen Majalisun dokokin Algeria

A ƙasar Algeria jamiyu uku waɗanda ke da alaka da shugaban ƙasar Abdulaziz Boutaflika sun cigaba da rike matsayin da suke da shi na rinjaye a majalisar dokokin. A sanarwar da ya bayar Ministan cikin gida Yazid Zerhouni yace jamíyar National Liberation Front (FLN) da jamíyar Democratic National Rally da kuma Society of Peace Movement baki daya sun sami kujeru 249 daga cikin adadin kujeru 389 na majalisar dokokin. Jamíyar yan ƙwadago mai tsatsauran raáyi ta sami kujeru 26 a zaɓen wanda ya gudana a ranar Alhamis inda ta zama babbar jamiyar adawa a majalisar dokokin.