Sakamakon Zaɓen Majalisar Dokokin Amirka | Siyasa | DW | 03.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon Zaɓen Majalisar Dokokin Amirka

Jam'iyyar Democrat ta shugaba Barak Obama ta yi asarar zaɓen majalisar dokokin Amirka a zaɓen da aka gudanar jiya talata

default

Zauren majalisar dokokin Amirka

Kamar dai yadda aka yi hasashe tun da farko 'yan jam'iyyar Republicans sun samu gagarumar nasara a zaɓen majalisar dokokin da aka gudanar a Amirka jiya talata, inda suka samu ƙarin kujeru 59. Sai dai kuma ko da yake sun samu nasara a zaɓen majalisar dattawa, amma har yau jam'iyyar Democrats ta shugaba Obama ce ke da rinjaye.

Obama / USA / Kongresswahlen

Shugaba Barak Obama a yaƙin neman zaɓe

Sakamakon zaɓen dai tamkar wani babban naushi ne a fuskar shugaba Obama, shekaru biyu kacal bayan ɗarewarsa kan karagar mulki. A wajejen ƙarfe tara na yamma a agogon gaɓar gabashin Amirka tashar telebijin ta CNN ta ba da sanarwar nasarar da 'yan mazan-jiyan suka samu a zaɓen majalisar dokokin Amirka.

John Boehner, kakakin wakilan jam'iyyar Republicans a majalisar dokoki, daga bisani yayi nuni da cewar sakamakon zaɓen wani babban saƙo ne ga shugaba Obama domin ya canza salon kamun ludayinsa. Kazalika jami'in siyasar na 'yan mazan-jiya ya bayyana shirinsa na ba da haɗin kai ga shugaba Obama sannan yayi nuni da cewar:

"Sabon rinjayen da muke da shi zai gabatar da wani sabon mataki, wanda babu ɗaya daga cikin jam'iyyun siyasar da suka haɗa da Democrats da kuma Republicans da tayi yunƙurin ɗauka a birnin Washington. Matakin zai fara ne da ƙayyade yawan abin da gwamnati ke kashewa da rage yawan jami'an gwamnati da yi wa majalisar dokoki garambawul domin sake danƙa wa Amirkawa alamuran gwamnati."

Wannan nasarar ta 'yan Republicans ta zo ne a daidai lokacin da al'amura suka fara kai wa jama'a iya wuya a game da yadda Obama ke tafiyar da al'amuran tattalin arziƙin Amirka, inda ake fama da yawan marasa aikin yi da ya kama kashi 9.6%. Kuma ainihin wannan matsalar ita ce ta taka muhimmiyar rawa a zaɓen. Su ma 'yan jam'iyyar Tea-Party dake da tsattsauran ra'ayin mazan-jiya zasu samu wakilcin Marco Rubio daga Florida da Rand Paul daga Kentucky a majalisar dattawa. Sai dai ba a san irin tasirin da jam'iyyar zata iya yi akan 'yan Republicans ba. Ita dai jam'iyyar tana ɗaukar kanta a matsayin wata ƙungiya ce ta adawa da gwamnati da tsaffin jam'iyyun siyasar Amirka kuma kawo yanzu 'yan takararta na amfani ne da tutar Republicans. To ko ya-Alla nan gaba za a samu wani rukuni ne na wakilan jam'iyyar Tea Party a majalisar dattawan? Ga dai abin da wakilinta Rand Paul yake cewa:

"In don ni ne sai in ce i ƙwarai kuwa. Kuma tun da sanyin safiyar gobe zan fara kai da komo akan wannan manufa."

A dai halin da ake ciki yanzu tuni shugaba Obama ya tuntuɓi John Boehner da Mit McConnell, gaggan wakilan Republicans a majalisar dattawa domin bayyana musu shirinsa na haɗin kai da su domin cimma wata madafa, wadda zata taimaka Amirka ta samu ci gaba a kuma kyautata makomar jin daɗin rayuwar al'umar ƙasar.

Mawallafi: Christina Bergmann/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu