Sakamakon zaɓen majalisar ƙananan hukumomi a Afrika ta kudu | Labarai | DW | 04.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaɓen majalisar ƙananan hukumomi a Afrika ta kudu

Shugaban ƙasar Afrika ta kudu Tabon Mbeki, ya bayyana matuƙar gamsuwa, ga nasara da jam´iyar sa, ta ANC ta samu, a zaɓen yan majalisun ƙanana hukumomi, da aka yi, ranar laraba da ta wuce.

Sakamakon wucin gadi na wannan zaɓe, ya ba ANC fiye da kashi 66 bisa 100, na jimillar ƙuri´un da aka kaɗa.

Tabon Mbeki, ya yabawa magoya bayan wannan jam´iya da kamin zaɓen, kafofin sadarwa su ka yi ta, yayata cewar al´umma ta ƙaurace mata.

Jam´iyar adawa ta DA, da ke sahu na 2, na da kimanin kashi 15 bisa 100, na jimmilar ƙuri´un .

Nan gaba a yau , a ke sa ran, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana sakamakon ƙarshen na zaɓen.