Sakamakon zaɓen ƙasar Beljium | Siyasa | DW | 14.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon zaɓen ƙasar Beljium

'Yan awaren Flemish a ƙasar ta Beljium suka lashe zaɓen na 'yan majalisun dokokin ƙasar

default

Rikicin siyasar Beljium bayan zaɓe

To sai dai har yanzu suna buƙatar samun goyon bayan wasu jam'iyyun siyasar domin kafa gwamnatin abin da ka iya ɗaukar dogon lokaci wanda kuma zai iya zama ƙalubale ga ƙasar a daidai lokacin da ta ke shirin karɓar shugabancin ƙungiyar Tarayya Turai.

Bayan kammala kidayar ƙuri'u kwata kwata a sakamakon zaɓen da ofishin ministan cikin gida na ƙasar ta Beljium ya bayyana ya nuna cewa ƙawancen jam'iyar Flamande na Bart de Wever ya samu kujeru 27 bisa 150 a majalisar wakilai.

Sannan sai jam'iyar 'yan gurguzu ta Wallon da kujeru 26 a gaban 'yan Liberaux masu magana da harshen Faransanci da suka samu kujeru 18 sai Social Democrat CDV masu kujeru 17.

Wannan nasara dai da 'yan Flamande ɗin suka samu wadda suke da ra'ayin ɓallewa tare da 'yan Dutch zuwa Tarayya Turai na zaman wani babban koma baya ga 'yan Walloniya wato al'umar kudancin Beljium masu magana da harshen Faransanci wanda kuma akasarinsu masu ƙaramin ƙarfi ne da suka dogara da arewacin ƙasar.

Mista De Bart De Wever shugaban jam'iyar NVA ta sabon ƙawance Flamande ya shaida cewa inda rana ta fito to tahin hannu ba zai iya kareta ba.

"Komai mai yiwuwa ne indai da akwai niya kuma wannan nasara da mu ka cimma a bayyane take ƙarara yankin arewacin na kan hanyarsa ta rabuwa da yankin kudancin wanda ke yawan tatsarmana da arziki."

A ranar ɗaya ga watan Yuli ne dai ya kamata ƙasar ta Beljium ta karɓi shugabancin ƙungiyar Tarayya Turai na karɓa karɓa, to sai dai masu lura da al'amuran yau da gobe na hasashen cewa wannan al'amari ya na zaman ƙalubale ga ƙasar da ma ƙungiyar Tarayya Turai, domin kuwa ba a tsammanin kafin ɗaya ga watan na Yuli za a kafa gwamnati a ƙasar ta Beljium saboda sarƙaƙiyar siyasar da ake ciki sannan kuma ga maganar wahaloli na tattalin arziki.

Abin da ake gani ko masu saka jari da manyan bankunan da ke bayar da basussuka ba za su iya haƙurin jira ba inda har zuwa watan Satumba ba a kafa gwamnatin ba.

Ruft Elio Die Rupo shi ne shugaban jam'iyyar 'yan Socialist.

"Abinda ya fi muhimmanci shi ne kamar yadda na riga na faɗa a samu maza da mata da suke da shirin tattaunawa domin samun wata yarjejeniya."

Tsofuwar gwamnatin Yves Lantemme dai ta yi marabus ne a cikin watan Afrilu da ya gabata a sakamakon wani ciƙas da aka samu akan wata mazaɓar da ake jayayya a kai da ya kawo tsaiko akan harkokin ƙasar.

A yanzu dai babbar ayar tambayar da masu fashin baƙi akan al'amuran siyasa suke yi akan wannan rikita rikitar siyasa da aka shiga a ƙasar ta Beljium wacce ke da al'uma mai yawan miliyan 6.5 masu magana da harshen Dutch da kuma masu magana da harshen Farasanci miliyan fuɗu ko wace makoma za su dosa.

A daidai lokacin da ƙasashen Turai ke fama da matsalar tattalin arziki da ta ratsa ƙasar Girka wacce ta ke barazana ga sauran ƙasashen Turai, shin ko sakamakon wannan rikicin siyasa da ƙasar ke fama shi ta kan iya samun kan ta a cikin irin matsalar ta tattalin arziki? Lokaci na gaba kaɗai zai iya tabattar mana da gaskiyar lamarin.

Mawallafi: Abdurrahmanne Hassane

Edita: Mohammad Nasiru Awal