Sakamakon zaɓe a Sierra-Leone | Labarai | DW | 24.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaɓe a Sierra-Leone

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a ƙasar Sierra Leone, ta bada sakamakon tagwayen zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki, wanda su ka wakana ranar 11 ga watan da mu ke ciki.

Kamar yada alƙalluman farko su ka nunar, jama´iyar adawa ta APC ta samu rinjaye a wannan zaɓe, tare da lashe kujeru 59, daga jimilar kujeru112 da majalisar ƙasar ta ƙunsa.

Jam´iyar SLPP ta shugaban ƙasa mai barin gado, Ahmed Tijani Kabba, ta tashi da kujeru 43, sai kuma jam´iyar PMDC ta sami kujeru 10.

A ɓangaren zaɓen shugaban ƙasa, babu ɗan takara da ya sami nasara a zagayen farko.

A game da haka, ya zama wajibi a shirya zagaye na 2, nan da makwani 2 masu zuwa.

Za a kara tsakanin ɗan takara jam` iyar adawa ta APC, Ernest Bai Koroma, da ya samu kashi 44, 3 bisa 100, a zagaye na farko, da kuma mataimakin shugaban ƙasa Solomon Barewa, da ya samu kashi 38,3 cikin100.

Ɗan takarar da yazo sahu na 3, ya riga ya bada goyan baya ga Bai Koroma na jam´iyar adawa.