Sakamakon zaɓe a ƙasar Uganda | Labarai | DW | 25.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaɓe a ƙasar Uganda

Shugaban ƙasar Uganda Yoweri Museveni ya kama hanyar lashe zaɓen da aka gudanar a ƙasar da gagarumin rinjaye. Zaɓen shi ne karo na farko bisa tsarin jamíyu da dama a tsawon shekaru 25 a tarihin ƙasar. Yayin da ya zuwa yanzu aka ƙidaya kusan kashi 91 cikin dari na yawan kuriún, hukumar zaɓe ta ƙasar ta baiyana cewa Museveni ya sami kashi 61 cikin ɗari na adadin ƙuriún yayin da abokin hamaiyar sa Kizza Besigye yake da kashi 36 cikin ɗari. A wani lokaci a yau ne hukumar zaɓen zata baiyana cikakken sakamakon. A waje guda dai madugun adawar Kizza Besigye yayi barazanar yin watsi da sakamakon zaɓen yana mai cewa an tafka magudi sosai a cikin sa. Jamiái na kasa da kasa wadanda suka lura da yadda zaɓen ya gudana sun baiyana cewa zaɓen ya gudana bisa adalci. Shi dai Yoweri Museveni ya shafe tsawon shekaru 20 yana shugabancin ƙasar Uganda.