1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓen yan majalisu a jihohi 2 na Jamus

September 18, 2006
https://p.dw.com/p/Buj9

An bayyana sakamakon zaɓen yan Majalisun jihohi 2, na ƙasar Jamus da aka gudanar jiya lahadi.

Jihohin sun haɗa da Berlin babban birninTarayya, da kuma Mecklemburg-Pomerania, da ke arewa maso gabancin ƙasar.

Wannan zaɓe na matsayin zakaran gwajin dafi, ga haɗin gwiwar jama´iyun CDU da SPD, da ke riƙe da ragamar mulki.

Jihar Mecklemburg-Pomerania, da ke matsayin ɗaya, daga wuraren da jam´iyar CDU, ta Angeller Merkell ta samu karɓuwa, na sahun ƙarshe, ta fannin ci gaba, idan a ka jera jihohin 16 da Jamus ta mallaka.

A Berlin inda SPD ta samu kashi 31 da dudu 2 bisa 100 na yawan kuri´un da a ka jefa, a yayin da CDU ta samu kashi 21 da dugu 6.

Wannan na matsayin sakamako mafi muni da jamiýar Angeler merkell ta samu a birnin Taraya a tsawan tarihin ta.

Jami´yar the Greens ta samu kashi kussan 14 a birnin Berlin, abinda ke matsayin gagaramar nasara a gare ta.

A jihar Mecklemburg-Pomerania jam´iyun SPD a wani mataki na ba zata, ta zarta CDU da yawan ƙuri´u, sai kuma jami´yar yan Nazi ta NPD da ta samu fiye da kashi 6 bisa 100.