1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasar DRC

November 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bube

Hukumar zaɓe mai zaman kanta,a Jamhuriya Demokradiyar Kongo ,ta bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa zagaye na 2 a hukunce.

Shugaban ƙasa mai yanzu, Joseph kabila, ya lashe zaɓen da kashi 58 bisa 100, a yayin da ɗan takara na 2, wato Jean Pierre Bemba, ya tashi da kashi kussan 42 bisa 100 na yawan ƙuri´un da aka kaɗa.

Saidai Bemba, yayi wasti da wannan sakamako, da ya ce an tabka maguɗi a cikin sa, ya kuma ambata bin hanyoyin doka, da su ka dace, domin ƙwatar yancin sa.

Wani mai magana da yawun ɗan takara da ya sha ƙasa, ya ce ba su da aniyar tada hankulla, ko da, haƙar ba ta cimma ruwa,ba bayan ƙaran da za su shigar a kotu ƙoli, to saidai sun gitta babban sharaɗi, na tabatar da tsaron Jean Pierre Bemba.