Sakamakon wucin gadi na zaɓen Australiya | Labarai | DW | 21.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon wucin gadi na zaɓen Australiya

Firaminista Julia Giilard ta kama hanyar lashe zaɓen gaba da wa'adi da ya gudana a wannan asabar.

default

Firaminista Julia Gillard ta Australiya

A ƙasar Australiya, ƙididdigar da aka gudanar bayan rufe runfunan zaɓe ta nunar da cewa firaminista Julia Gillard mai ci a yanzu ta samu nasarar yin tazarce, sakamakon ƙwarya-ƙwaryar rinjaye da ta samu a zaɓen 'yan majalisa da ya gudana a wannan asabar.

Tasoshin talabijin da aka fi ji da su a ƙasar wato Channel 9 da kuma Sky News sun sanar da cewa, 'yar takarar da ta tsaya ƙarƙashin jam'iyar Labour ta lashe kashi 51% zuwa 52% na ƙuri'n da aka kaɗa. Yayin da madugun 'yan adawa wato Tony Abbott da ya tsaya ƙarƙashin inuwar jam'iyar Liberal, ya lashe kashi 48% na ƙuri'un.

Gobe da lahadi ne za a samu cikekken sakamakon zaɓen na gaba da wa'adi, da kuma ke zama mafi sarƙaƙiya na shekaru 70 da suka gabata a ƙasar ta Australiya. Mutane miliyon 150 ne su ka kaɗa ƙuri' a ƙasar ta Australiya , da nufin sabonta kujeru 150 na majalisar dokoki da kuma 76 na majalisar dattijai.

Julia Gillard da ke zama mace ta farko da ta shugabanci gwamnati, ita ta bukaci a gudanar da zaɓen na gaba da wa'adi a daidai lokacin da taurarinta ke haskawa. Amma kuma rashin karɓuwar da wasu manufofinta ba su yi ba a tsakanin al'uma, ya kawo mata cikas a zaɓen.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Zainab Mohammed Abubakar