Sakamakon wucin gadi na zaɓen Australiya
August 21, 2010A ƙasar Australiya, ƙididdigar da aka gudanar bayan rufe runfunan zaɓe ta nunar da cewa firaminista Julia Gillard mai ci a yanzu ta samu nasarar yin tazarce, sakamakon ƙwarya-ƙwaryar rinjaye da ta samu a zaɓen 'yan majalisa da ya gudana a wannan asabar.
Tasoshin talabijin da aka fi ji da su a ƙasar wato Channel 9 da kuma Sky News sun sanar da cewa, 'yar takarar da ta tsaya ƙarƙashin jam'iyar Labour ta lashe kashi 51% zuwa 52% na ƙuri'n da aka kaɗa. Yayin da madugun 'yan adawa wato Tony Abbott da ya tsaya ƙarƙashin inuwar jam'iyar Liberal, ya lashe kashi 48% na ƙuri'un.
Gobe da lahadi ne za a samu cikekken sakamakon zaɓen na gaba da wa'adi, da kuma ke zama mafi sarƙaƙiya na shekaru 70 da suka gabata a ƙasar ta Australiya. Mutane miliyon 150 ne su ka kaɗa ƙuri' a ƙasar ta Australiya , da nufin sabonta kujeru 150 na majalisar dokoki da kuma 76 na majalisar dattijai.
Julia Gillard da ke zama mace ta farko da ta shugabanci gwamnati, ita ta bukaci a gudanar da zaɓen na gaba da wa'adi a daidai lokacin da taurarinta ke haskawa. Amma kuma rashin karɓuwar da wasu manufofinta ba su yi ba a tsakanin al'uma, ya kawo mata cikas a zaɓen.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar