1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon taron Yamoussoukro

Yahouza SadissouMarch 1, 2006

Ɓangarori masu gaba da juna a Cote D´ivoire sun kammalla zaman taro a Yamoussoukro.

https://p.dw.com/p/Bu1N

Tun ɓarkewar rikicin tawaye a Cote d`ivoire, yau da kussan shekaru 4, da su ka wuce, wannan shine karro na farko, da a kayi ganawar ƙeƙe da ƙeƙe a cikin ƙasar Cote D´Ivoire, tsakanin, shugaban ƙasa Lauran Bagbo, da shugaban adawa Allasan Watara, da na yan tawaye Guillaume Sorro, da kuma tsofan shugaban ƙasa Henri Konan Bedie, bisa gayyatar praministan riƙwan ƙwarya Charles Konnan Banny.

Bayan sa`o `i 4, su na tantanawa sun fido da sanarwar ƙarshen taro, wace a cikin ta su ka bayyana buƙatar haɗuwa lokaci zuwa lokaci, cikin fahintar juna,domin masanyar ra´ayoyi ,a game da harakokin da su ka jiɓanci tafiyar ƙasa.

Sun kuma bayana amincewa da zaben membobin hukumar zaɓe mai zaman kanta, da zata shirya zaɓɓukan da za a gudanar a watan Oktober mai zuwa.

Kazalika, sun yi na´am da alƙalancin wakilin mussamman na Majalisar Dinkin Dunia, Antonuo Montero, a game da abinda ya shafi zaɓen.

Sannan sun cimma daidaioo a kan wajibcin ƙirƙiro kujera mataimakin shugaba na 4, a cikin hukumar zaɓe mai zaman kanta.

A game da rijistan jama´a ɓangarorin sun amince su gudanar da wannan aiki cikin hadin gwiwa.

A dangane da kawnce ɗamara yaƙin tawaye, shuwagabanin sun jaddada matsayin da a ka cimma a tarrurukan sulhu ,da su ka gabata, a kan cewar tawagogin tawaye da na sojoji masu biyaya ga gwamnati, su zauna tebrin shawara domin tsara mattakan kwance makaman.

A yayin da ya ke bayyani, jim kadan bayan taron Praministann Charles Konnan Banny, ya bayyana wannan haɗuwa da babban mataki, ta fanning maido da zaman lahia a Cote D´Ivoire, mussaman ta la´akari da yadda, magabatan 5, su ka a mince su bada hadin kai don shirya zaɓen shugaban ƙasa a cikin wa´adin da Majalisar Ɗinkin Dunia ta ƙayyade, wato a watan Oktober mai zuwa.

A nasu gefe kafofin sadarwa na ƙasa sun yi ta hurta albarkacin bakinsu, a game da sakamakon haɗuwar ta jiya.

Jaridar le Patriote mai alaƙa da adawa, ta rubuta cewa Praminista ya cencenci yabo, a kan yada ya samu nasara haɗa wannan mutane 4 wuri guda, kuma a cikin kasar Cote D´ivoire , abinda ba a taɓa gani ba, tun farkon wannan rikici.

Itakuwa, jaridar Fraternite Matin, da ta ke sharhi a game da taron ta ce, wannan shine karo na farko, da ɓangarori masu gaba da juna, a Cote D´ivoire su ka shirya taro, ba bisa jagorancin wani shugaban ƙasa ba, na ƙetare.

To badai girin girin ba ta yi mai, inji wannan jarida, domin so dayawa, wannan mutane sun sha ɗaukar alkawuran da ba su cikawa.

A nata ɓangare, jaridar Notre Voie mai alaƙa da gwamnati, ta yi Allah wadai da sanarwar ƙarshen taron, mussamman a game da passalin hukumar zaɓe mai zaman kanta, wadda a cewar jaridar, an tattara jagorancin hukumar cikin hannunwan adawa da yan tawaye.

Sannan wannan jarida na adawa da matakin girka rundunar ƙasa ta haɗin gwiwa.