1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon taron shawarwari a Annapolis

Israila da Larabawa sun amince da sake komawa zauren shawarwarin neman sulhunta tsakiyanin su a yankin Gabas ta Tsakiya

Shugabannin Israila da na Palesɗinawa yau a Annapolis, sun cimma daidaituwa a game da sake komawa shawarwarin neman zaman lafiya da aka daɗe da dakatar dasu, bisa manufar ƙirƙiro yantacciyar ƙasar Palesɗinawa ya zuwa ƙarshen shekara mai zuwa. Wata sanarwa ta haɗin gwiwa da shugaban Amerika George Bush ya karanta, ta nuna cewar Pirayim ministan Israila, Ehud Olmert da shugaban Palesɗinawa Mahmud Abbas sun yi alƙawarin fara shawarwari masu tsanani tsakanin su tun a wata mai zuwa, wanda shine karo na farko tsakanin ɓangarorin biyu a tsawon watanni bakwai.

Sanarwar da shugabannin na Israila da Palesɗinbawa suka bayar a karshen taron ƙolin da suka yi a Annapolis tace duka ɓangarorin biyu suna baiyana karfin zuciyar su game da kawo ƙarshen zubar da jini da shekaru masu yawan gaske na zaman wahala da gaba tsakanin al’ummomin su, sun kuma baiyana shirin shigar da wani sabon zamani a yankin na gabas ta tsakiya, dake tattare da zaman lafiya, kwanciyar hankali yanci, tabbatar da tsaro, kiyaye shari’a da mutunta juna tare da amincewa da wanzuwar juna, sai kuma zaman tare, kafaɗa da kafaɗa ba tare da yaki ko wani tashin hankali ko gwada karfi ba. Kazalika, shugabannin biyu sun yi alƙawarin hada gwiwa domin fuskantar matsalar aiyukan tarzoma ko yan tarzoma tsakanin su.

Taron na Annapolis, kusa da birnin Washington, shugaban Amerika, George Bush ya gaiyace shi, inda a bayan Ehud Olmert na Israila da shugaban Palesɗinawa Mahmud Abbas, sauran wadanda suka halarce shi, sun haɗa har ƙasashe 44, ciki har da wakilan ƙasashen Larabawa 14 sha da hudu.

Lokacin da ya baiyana gaban manema labarai a ƙarshen taron, shugaban Amerika, George Bush yace:

Wakilan gwmanatin Israila da na ƙungiyar Paleasɗinawa, ƙarƙashin jagorancin Pirayimn minista Ehud Olmert da shugaba Mahmud Abbas a matsayin sa na shugaban ƙungiyar PLO, karkashin jagorancin shugaba George Bush tare da goyon bayan sauran wakilan ƙasashen duniya, sun cimma daidaituwa kann manufar kawo ƙarshen wahalolin da al’ummomin su suka dade suna fama dasu. Zasu fara shawarwari nan gaba kaɗan, kuma sun amince game da saduwa tsakanin su ko wane mako biyu tun daga ranar 12 ga watan Disamba. Waɗannan shawarwari zasu ci gaba, sai idan an cimma wani tsarin dabam, amma shawarwarin na neman zaman lafiya za a yi ne bisa manufar aiwatar da shirin neman zaman lafiya da ake kira Road Map, kamar yadda Amerika ta tsara.

Pirayim mministan Israila, Ehud Olmert yace wadannan shawarwari da za’a kaddamar a wata mai zuwa, zasu nemi warware dukkanin sauran matsalolin da suka rage a tsakanin Israila da Palesdinawa.

To sai dai kuma shugabannin na Israila da na Palesdinawa duka suna fama da rauni a manufofin su na cikin gida. Wani mai magana da yawun kungiyar Hamas, wadda ta mamaye yankin Gaza yace kungiyarsa tayi adawa da zaman taron kolin na Annapolis ne saboda wnanan taro ba komai bane illa bata kokaci kawai. TO amma ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier ya yabi sakamakon da aka samu a zauren taron, inda yace:

Idan har a nan aka sami nasarar shimfida sharuddan da suka dace yadda zaman za’a sulhunta rikicin gabas ta tsakiya ya zuwa karshen shekara kamar yadda suka bangarorin biyu suka yi alkawari, to ashe uwa mafarkin mku zai tabbata, kann cewar Israila eda Palesdinawa zasu zauna kafada da kafada cikin kwanciyar hankali a matsayin makwabtan juna.

Palesinawa suna da sharuddan da suka shimfida tare da goyon bayan kasashen Larabawa kafin zaman lafiya ya samu tsakanin su da Israila. Daga ciki har dfa tabbatar da hadin kann birnin KUdus a matsayin hedikwataer mulkin duk wata yantacciyar kasar Palesdinawa da za’a kirkiro a yankin na gabas ta tsakiya.