Sakamakon taron ministocin cikin gida ma ƙasashen EU a birnin London | Labarai | DW | 17.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon taron ministocin cikin gida ma ƙasashen EU a birnin London

A sakamakon taron yini ɗaya da su kira jiya, a birnin London na Engla, ministocin harakokin cikin gida, na ƙungiyar gamaya turai, sun bayana ɗaukar matakan haɗin gwiwa, domin yaƙi da ayyukan ta´adanci.

Taron ya biwo bayan yunƙurin shirya ta´adanci, da jami´an tsaron Britania su ka bankaɗo, a kan jirage masu zirga zirga, tsakanin Britania da Amurika.

Ministocin sun haƙiƙance cewar, dunia na ci gaba da fuskantar barazanar ta´danci ,a game da haka, ya zama wajibi ga ƙashen turai, tare da taimakon dukan sauran sassa na dunia, su gama ƙarfi, domin yaƙar al´amarin.

Ministocin, sun bayana hanyoyin 4 na cimma wannan buri, wato riga kafi, kariya, bincike mai zurfi,da kuma hukunci mai tsanani.

Sannan, sun yanke shawara ƙarfafa masanyar labarai a kan hanyoyin da a ke anfani da su, domin rijistan yan tarzoma a cikin makarantu, wuraren ibada, da ta hanyar Internet.

A game da wannan matakai na haɗin gwiwa Ministan harakokin cikin gida na Britania, John Red ya bayana cewar:

„Ya na da matuƙar mahimmanci, mu dinga masanyar hanyoyin yaƙi da ta´danci, tsakanin ƙasashen mu, domin dukkan mu, bori guda ne, mu ke ma tsafi ,wato kare lahiar al´ummomin mu“.