1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon taron makomar siyasar kasar Mauritania

October 31, 2005
https://p.dw.com/p/BvN9

A kasar Mauritania wakillai fiye da 500 na jam´iyun siyasa da na kungiyoyi masu zaman kansu, sun kammala zaman taron shawarwari, a game da makomar siyasa kasar.

Shugaban komitin adalci da demokradiya, wato shugaban kasa Ely Muhamed Uld Vall ,ya gayyaci wannan taro, a shirye shiryen maida Mauritania bisa tafarkin Demokradiya, bayan juyin mulkin da a ka gudanar a watan Ogust da ya wuce.

A sakamakon wannan taro wakilai sun amince da shawarwarin da gwamnatin ta gabatar.

Za a fara zabbuka a watan juni na shekara ta 2006 a kammala da zaben shugaban kasa ranar 24 ga watan juni na shekara ta 2007.

Sun tsaida wa´adin mulkin shugaban kasa a tsawon shekaru 5 da damar yin tazarce karro daya.

Kazalika sun cimma daidaito na girka hukumar zabe mai zaman kanta, mai cikkaken mulki, da kuma dokoki na inganta yanci da walwalar jama´am, ba tare da nuna wariyar launin fata ko ta kabila ba.