Sakamakon taron larabawa a Libiya | Labarai | DW | 28.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon taron larabawa a Libiya

Shugabanin ƙasashen larabawa sun kammalla taron ƙoli na yini biyu a birnin Syrte na ƙasar Libiya

default

Ƙarshen taron ƙolin shugabanin ƙasashen larabawa

Shugabanin ƙasashen larabawa sun kammalla zaman taron ƙoli na yini biyu da suka shirya a birnin Syrte na ƙasar Libiya.Rikici tsakanin Isra´ila da Palestinu na daga batutuwan da suka mamaye ajendar taron.

A sakamakon wannan taro shugabanin sun yanke shawara dakatar da tattanawa da Isra´ila muddun ba ta daina gine gine a gabacin birnin Qudus ba.Sannan shugabanin,sun yi kira ga shugaban ƙasar Amurika Barak Obama ya cigaba da matsawa hukumomin bani yahudu  ƙaimi, har sai sun dakatar da mamayen yankunan Palestinu.

A yayin da ya ke huruci game da sakamakon taron Saeb Erekat na tawagar Palestinu ya bayyana gamsuwa:

"Ƙasashen larabawa da gaske suke yi, sun kuma yi kira da babbar murya ga Isra´ila ta shiga taitayinta.Larabawan sun gaji da take-take da kuma mayar da hannun agogo baya da Isra´ila ke yi."

A ɗaya ɓangaren shugaban ƙasashen larabawa sun yanke shawara sake kiran wani taro na mussamman kamin ƙarshen watan Oktober, domin bitar inda aka kwana game da rikicin Gabas ta Tsakiya.Sannan zasu tunanin faɗaɗa Ƙungiyar ga wasu ƙasashen musulmi maƙwabta wanda ba na larabawa ba, kamar Iran da Turkiyya.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita:Halima Balaraba Abbas