Sakamakon Taron Kolin Shuagabannin Kasashen Spain, Faransa Da Jamus | Siyasa | DW | 14.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon Taron Kolin Shuagabannin Kasashen Spain, Faransa Da Jamus

A yammacin jiya litinin ne shuagabannin kasashen Spain da Faransa da Jamus suka kammala ganawarsu ta koli a birnin Madrid tare da alkawarin yin bakin kokarinsu wajen ganin an albarkaci daftarin tsarin mulki bai daya na kasashen Turai a cikin gaggawa.

Shuagabannin kasashen Jamus da Spain da Faransa

Shuagabannin kasashen Jamus da Spain da Faransa

P/M Spain Jose Luis Zapatero ya sha tafi da guda lokacin da ya furta cewar bisa ga dukkan alamu tsofuwar nahiyar Turai ta fara rikidewa domin zama budurwa. Da wannan furucin, wanda tamkar hannunka mai sanda ne ga masu zargin wani bangare na nahiyar da bin wani tsofon yayin da aka dawo daga rakiyarsa, P/M kasar ta Spain ya sosa wa mutane daidai wurin dake yi musu kaikai. Domin kuwa a yayinda magabacinsa Jose Maria Aznar ya fi karkata zuwa ga shugaban Amurka George W. Bush da P/M Birtaniya Tony Blair, shi Jose Luis Zapatero, bayan da ya dare kan karagar mulki, bai yi wata-wa ba wajen neman kusantar kasashen Jamus da Faransa bisa manufar sake dawo da kasar Spain a cikin zuciyar nahiyar turai, kamar yadda yayi bayani. A nasu bangaren Schröder da Chirac, ba su yi dari-dari ba wajen ba wa Zapatero goyan baya a game da na’am da yake yi da daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashen Turai. Swchröder ya ce gwamnatin Zapatero ta taka rawar gani wajen cimma tudun dafawa akan kudurin da aka zartas a game da daftarin tsarin mulkin akan suffarsa na yanzu. Dukkan kasashen na Spain da Faransa da Jamus na tattare da ra’ayin cewar wajibi ne dukkan kasashen Kungiyar Tarayyar Turai su albarkaci kudin a cikin gaggawa. A game da maganar karbar Turkiyya kuwa, baki ya zo daya tsakanin Zapatero da Chirac da kuma Schröder akan cewar wajibi ne kasar ta ci gaba da daukar sahihan matakai na garambawul, ko da yake sun hakikance da ire-iren ci gaban da ta samu bisa manufa. Kazalika dukkan jami’an siyasar sun bayyana goyan bayansu ga bin manufofin ketare bai daya tsakanin kasashen KTT, musamman ma dangane da kasar Iraki. Bisa ga ra’ayin P/M Spain za a cimma nasara ne a fafutukar murkushe ta’addanci tsakanin kasa da kasa idan an samu hadin kai a fannonin na shari’a da tsaro da ayyukan leken asiri da sauran batutuwa na siyasa ta yadda ba za a wayi gari maganar gwagwarmayar yada angizon al’adu ta tabbata gaskiya ba. A halin yanzu haka an cimma daidaituwa tsakanin kasashen Jamus da Spain da Faransa akan karfafa hadin kan manufofinsu na yakar miyagun laifuka. To sai dai kuma duk da wannan daidaituwar da aka samu a tsakanin kasashen uku, akwai inda take kasa tana dabo kuma nan ba da dadewa ba sabaninsu zai fito fili. Wannan maganar dai ta shafi kaso na tallafin da kasashen KTT ke samu, inda kasar Spain a matsayinta na mai cin gajiyar wannan tallafi na kudi dake kan wani matsayin da ya banbanta da na kasashen Jamus da Faransa, wadanda ke kan gaba wajen ba da gudummawa mafi tsoka ga baitul-malin kungiyar. Dukkan kasashen uku dai zasu ci gaba da gudanar da irin wadannan tarurruka na hadin guiwa tsakaninsu, amma, kamar yadda Schröder ya nunar, ba makasudinsu ne su mayar da sauran kasashen kungiyar ta tarayyar Turai saniyar ware ba.