1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon Taron Kolin Shuagabannin Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai

June 21, 2004

A taronsu na yini biyu shuagabannin kasashen KTT sun cimma daidaituwa akan daftarin tsarin mulki bai daya tsakaninsu

https://p.dw.com/p/Bviq
Taron kolin KTT a Brussels
Taron kolin KTT a BrusselsHoto: AP

Duk da yarfe gumi da aka sha famar yi amma a karshe kwalliya ta mayar da kudi sabulu, inda shuagabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai suka cimma daidaituwa akan daftarin tsarin mulki bai daya tsakaninsu. Bisa ga dukkan alamu kuwa, wani abin da ya taimaka aka cimma wannan manufa ta tarihi shi ne ko oho da akasarin mazauna kasashen kungiyar suka yi da zaben wakilan majalisar Turai da aka gudanar baya-bayan nan. Kuma duk da sarkakiyar dake tattare da kundin wajen fahimtar abubuwan da ya kunsa, amma wannan daidaituwa da aka cimma tana da muhimmanci wajen tafiyar da al’amuran kungiyar tarayyar Turai dake ci gaba da bunkasa. Rabon ayyuka da za a yi a tsakanin kafofin dabam-dabam na kungiyar zai taimaka kowa-da-kowa ya fahimci alkiblar da aka fuskanta. To sai dai kuma sigar aiwatar da kudurorin daftarin tsarin mulkin ce zata ba da haske a game da tasirinsa a zukatan jama’a. An dai saurara daga bakin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder yana mai fada jim kadan bayan taron kolin cewar daftarin tsarin mulki kadai ba zai wadatar wajen tasiri a zukatan jama’a ba, saboda babu wani canjin da zai samar ga harkokin rayuwarsu ta yau da kullum. Amma akalla abin madalla shi ne hadin kan da aka samu tsakanin illahirin kasashen kungiyar su 25 domin cimma wata manufa mai sassauci. Abu daya da ya gurbata yanayin taron kolin ya kuma sanya murna ta koma ciki dangane da wannan kyakkyawan ci gaba da aka samu shi ne gazawar da shuagabannin suka yi wajen cimma daidaituwa akan wani mutum daya da zai gaji mukamin shugabancin hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayyar Turai Romano Prodi. A sakamakon wannan gazawar aka tsayar da shawarar gudanar da wani taron koli na musamman domin zaben magajin Prodi mai barin gado. Sabani da gardandamin da aka fuskanta a tsakanin shuagabannin kasashen bisa dalilai na banbancin ra’ayin siyasa yayi daura da sibgar da ake fatan ganin kungiyar ta tafiyar da ayyukanta. A karkashin daftarin tsarin mulkin na bai daya dai, nan gaba majalisar Turai ce zata kada kuri’ar raba gardama domin nadin shugaban hukumar zartaswa ta kungiyar. A yanzun dai bayan daidaituwar da aka cimma akan daftarin tsarin mulki sai kuma a sa ido aga yadda zata kaya a kasashen dake da dimbim masu adawa da manufofin hadin kan Turai, kamar Birtaniya, Irland, Poland da Denmark, lokacin da al’ummominsu zasu kada kuri’unsu na raba gardama akan kundin tsarin mulkin. Hatta a kasar Netherlands, mai yiwuwa mutane su kada kuri’ar kin yin na’am da daftarin tsarin mulkin saboda angizon da Jamus ta nuna wajen hana shawarar da kasar ta bayar game da tsaurara kudurorin yarjejeniyar nan ta kawancen zaman lafiya da kasashen gabacin Turai. Mai yiwuwa nan gaba murna ta koma ciki dangane da wannan nasara ta gajeren lokaci da Jamus ta samu wajen toshe wannan manufa ta kasar Netherlands.