1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon taron G8 da G20

Shugabannin manyan ƙasashen duniya da suka kammala taro a Kanada, sun amince da kyawtata bunƙasar tattalin arziki da samar da aikin yi.

default

Shugabannin ƙasashen G20

Shugabannin ƙasashen da sukafi ƙarfin tattalin arzikin da masana'antu, sun kammala taronsu wanda aka fi sani da G20. Taron da ya gudana a birnin Toronto dake ƙasar Kanada, ya samu amincewar shugannin bisa ɗaukar matakai na rage basussuka dake kansu.

Taron dai ya gudana a kashi biyu, inda da farko aka fara da taron ƙasashe takwas mafiya tattalin arzikin masana'antu wato G8, kana aka kammala shi da taron ƙasashe ashirin, mafiya ƙarfin tattalin arziki na duniya wato G20. Shugabannin sun yi mahawarori da dama, waɗanda suka haɗa manufar da Jamus ta je da ita na sakawa ribar da bankuna ki samu haraji da manufar Amirka na ƙara ƙason zaburar da tattalin arziki ƙasashen. Duk a ƙoƙarin shawo kan basukan da ke kan ƙasashen. Ƙasashen Turai dai sun bayyanawa taron cewa, abinda yafaru a Girka wani kyakkewan misaline ga kowa, kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana farin cikin ta bisa yadda taron ya gudana. Inda tace

Tsaida lokaci na rage giɓin da muke da shi izuwa shekara uku na gaba, da muaka yi, ya nuna afili wani tsarini mai ma'ana. Zamu ci gaba da tsuke bakin aljihu, wanda kuma mu ƙasashen da ke da ƙarfin tattalin arziki, zai ba mu damar rage basukan dake kanmu da kusan raɓi nan da shekara ta 2013. Wannan gagarumar nasarace, a haƙiƙa nasarar da aka samu ta wuce yada na zata. domin mun ɗau matakin cikin gaskiya. Kasancewa dukkan nin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki sun amince, a ganina wata nasara ce"

Shi dai shugaban ƙasar Amirka Barack Obama, ya nemi da sai ƙasashen Turai su ƙara yawan kason zaburar da tattalin arzikinsu, to hakan bata samu, inda ƙasashen Turai sukace babu wani kaso da za'a sake warewa. Don haka Obama yace a fili take muna da banbanicn ra'ayi amma duk manufarmu gudace.

Obama yace "Akwai saɓani wajen martanin da ƙasashen ke mayarwa, dalilin haka kuwa shine banbacin matsayin da ƙasashenmu ke da shi. Amma dai manufarmu tana fiskantar hanya gudu, wanda take nufin samarda tsari mai ɗorewa da zai samarwa mutanenmu aiki yi."

Bayan kammala taron mai masauƙin baƙi, Firimiyan ƙasar Kanada Stephen Harper, ya bayyana gamsuwa yadda daga bisani shugabbani suka samu matsaya guda. Inda yace

"Dukan shugabanni sun amince da cewa, ɗaukar matakin haɗen bagarorin kuɗi wuri guda, shi kaɗai ba zai wadatar ba, dole a samu cigaban aiwatar da tsarin bai ɗaya na gajeren lokaci, ta yadda muke bunƙasa tsarin da muka yi, haka  zamu tabbatar da ɗorewar dai daito wajen ci gaba"

Taron dai ya gamu da masu zanga zanga waɗanda ke ƙyamar tsarin da shugabannin ke yi. Inda suke zargin shugabannin suna ɗaukar waɗannan matakanne don son ransa kawai bawai don ci gaban ƙasashe matalauta ba.

A ɗaukacin makon dai dubban 'yan fafitika suka yi ta bore a kusa da inda ake taron, abinda kuma ya haddasa kame fiye da mutane ɗari biyar.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Henrik Böhme. Edita: Mohammad Nasiru Awal