1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

041111 G20 Gipfelabschluss

November 4, 2011

Bayan kwanaki biyu suna tafka mahaurori shugabanin G20 sun cimma matsaya guda wajen magance matsalolin kudi da wasu kasashe membobi ke fama da su

https://p.dw.com/p/135SG
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabanin kasashe masu karfin tattalin arziki na kungiyar G20 sun kammala zaman taron da suka shirya a birnin Cannes na kasar Faransa.Manyan batutuwan da suka tattana akai sun hada da matsaloli a kasashen dake amfani da takadar kudin Euro.

A tsawan yini biyu shugabanin kasashe da na gwamnatin kungiyar G8 sunyi masanyar ra´ayoyi game da matsalolin da kasashen ke fama da su hasali ma dai kasar Girka, wadda ta shiga kanun labaran duniya.

Kungiyar G20 ta bayyana karar cewar ba zata zuba ido kasar Girka ta fada bila´in kariyar tattalin arziki ba,wanda kuma zai iya bazuwa a sauran kasashen.

Duk da cewar Firaministan Girga George Papandreou ya yi watsi da batun shirya kuri´ar raba gardama game da fasalin kubutar da Girka da Tarayya Turai ta tanada,amma fa har yanzu kasar abun tsoro ce inji mahalarta taron G20.

Banda kasar Girka shima tattalin arzikin kasar Italiya ya fara nuna alamun yaushi inji shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, EU taza ta kara saka ido ga Italiya:

"Taron G20 ya tabbtar da wajibcin daukar matakan riga kafi.Hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayya Turai da Asussun Bada Lamuni na Duniya za su hada karfi domin kara bi sau da kafa halin da Kasar Italiya ke ciki".

A tsukin ko wane watani ukku hadin gwiwar kungiyoyin biyu zasu dinga gabatar da rahoto game da Italiya.

A daya bangaren, taron G20 ya yanke shawarra taimakawa wasu jerin bankunan da suka tsinci kansu cikin halin rai kwaikwai mutu kwakwai.

Sannan G20 zata kara ware kudade domin sakawa ga Asusun Bada Lamuni na duniya, wanda zai alkinta su ta fannin ci gaba kasashe.

Ta fannin nahiyar Afirka, Afrika ta kudu kadai ke matsayin memba a cikin rukunin kasashen G20, ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu yayi tsokaci game da moriyar da Afrika ka iya samu a wannan taro:

"Lalle matsalar kasashen da ke amfani da takardar kudin Euro ita ce ta mamaye taron, to amma an gabatar da kasidodi da laccoci game da cigaban kasashe masu tasowa musaman na Afrika, shaharraren mai kudinan Bill Gates, ya gabatar da wata kasida inda ya bayyana wasu jerin husa´o´in wanda zasu taimakwa a shayo kan matsalar talauci da Afrika ke famada shi".

A bilbishin matsalolin kariyar tattalin arziki ,taron G20 ya tattanawa game da batun farashen kayan abinci da ke tashin gobran zabi a duniya. Jörg Kalinski na hukumar dake kula da sa ido ga farashen kayan masarufi a tsokaci game da nasarar da ya ce an dan samu a taron:

"Ba lefin an samu dancigaba game da samar da abinci da waddatace da kuma yaki da karin farashe kayan masarufi.

To amma gaskiya a zahiri babu har yanzu da sauran rina kaba game da wannan batu."

Daya daga babar nasara da tarona na G20 ya cimma shine matakan cikin gida da sabin kasashe wanda a halin yanzu tattalin arzikin su ke bunkasa, wanda suka hada da China, Indiya da Brazil su ka yi alkawarin dauka da zumar taimkawa kasashe Turai su ceton tattalin arzikinsu da ya kama hanyar rugujewa.

A kasa,za ku iya sauraran rahoto da kuma sharhi game da taron na G20

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani