1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon Taron Duniya Akan Makomar Yanayi A Buenos Aires

Duk da cewar a ranar 16 ga watan fabarairu mai zuwa ne yarjejeniya Kyoto zata fara aiki, amma taron duniya akan makomar yanayin da aka kammala a Buenos Aires bai cimma wata nasara ta a zo a gani ba

Wakilin Amurka a zauren taron na Buenos Aires, Harlan Watson, ya bayyana mamakinsa a game da yadda ake shafa wa kasar kashin kaza a matsayin mai hana ruwa gudu ga manufofin kare makomar yanayin duniya. Amma fa a karshe magana ta fito fili a game da cewar kasar ta Amurka, lalle ita ce ke kafar ungulu ga duk wani ci gaban da ake fatan cimma a fafutukar kare makomar yanayin duniya. Domin kuwa dukkan yunkurin da kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da kuma kasashe masu tasowa suka yi na musayar yawu da kasar ta Amurka a game da yadda al’amura zasu kasance bayan kawo karshen aikin yarjejeniyar Kyoto a shekara ta 2012, ya ci tura, alhali kuwa kasar dake da kashi 5% kacal na al’umar duniya, ita ce ke da alhakin fitar da kashi 25% na gubar Carbondioxid dake haddasa dimamar yanayin duniyar. Ita ma Saudiyya ta fito karara tana mai kiran cike gibin kudadenta na shiga idan har ta fuskanci koma bayan cinikin man da take haka, lamarin da ya kara gurbata yanayin zauren taron na Buenos Aires. Dangane da kasashen Turai kuwa, sun shiga lalube ne a cikin dufu a game da sibgar ma’amallarsu zata kasance tare da Amurka akan manufar ta kare makomar yanayin duniya. Idan har zarafi ya kama kasashen zasu yi gaban kansu wajen daukar matakan da suka dace. Abu daya da ake tsoro shi ne ka da a wayi gari wasu daga cikin kasashen na Turai zasu nemi fakewa bayan Amurkan domin kin tabuka kome. Misali an saurara daga bakin ministan muhalli na kasar Italiya Altero Matteoli yana mai fadin cewar babu wani mataki na a zo a gani da za a iya dauka domin kare makomar yanayin duniya bayan shekara ta 2012, sai fa tare da tsoma hannun kasashen Amurka da Indiya da kuma China. Manufa a nan shi ne nan gaba a mayar da lamarin akan wata sibga ta radin kai ko wata yarjejeniya tsakanin kasashe biyu a maimakon yarjeniyoyi na gama gari. A takaice dai murna ta koma ciki ga wadanda suka shiga zauren taron tattare da kwarin guiwar cewar za a samu wani sabon jini ga manufofin kasa da kasa na kare makomar yanayin duniya ta la’akari da karatowar wa’adin fara aikin yarjejeniyar Kyoto daga sha shida ga watan fabarairu mai zuwa. Domin kuwa a mai makon haka akwai barazanar sake mayar da hannun agogo baya a fafutukar da ake yi na kayyade matsalar dimamar yanayin duniyar.