1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon taron Au a Accra

Sharhi kan batutuwan taron AU

Alpha Omar Konare

Alpha Omar Konare

Manufar da kungiyar gamayyar Afrika ta sanya a gaba wanda kuma aka tabka mahawara akai a taron da aka kammala a birnin Accran kasar Ghana shine yiwuwar kafa hadaddiyar daular kasashen nahiyar,tare da habaka tattalin arzikinta da inganta lamuran siyasa.

Sakamakon taron wanda aka gabatar dashi cikin daren jiya dai na nuni dacewa shugabannin kasashen na Afrika zasu cigaba da kokarin cewa haka ta cimma ruwa a dangane da wadannan manufofi nasu,har ya zuwa taron kungiyar na gaba da zaa gudanar a watan janairun shekara ta 2008,idan Allah ya kaimu.

Mai masaukin baki Shugaba John Kufuor ,wanda yaki bayyana matsayinsa dangane da wannan mahawara dai,ya jaddada bukatar bin matakan da suka cancanta wajen cimma wannan buri da suka sanya gaba

Alokacin gabatar da sakamakon wannan taro na yini ukun dai,shugaba Mammar Ghadaffi na Libya da Abdullaye Wade na kasar Senegal basa kan kujerunsu.

Ayayinda zaa cigaba da nazarin yiwuwar kafa hadaddiyyar daular kasashen Afrika,akwai kuma baukatar nazari dangane da matsalolin siyasa dana tattalin arziki da nahiyar ke fama dasu.

Wannan kungiya ta AU mai wakilan kasashe 53 a yau dai,bata da wani abun azo a gani data cimmawa da kafuwar ta bisa ga laakari da tarin matsaloli da take fama dasu kuma ta gaza warware kowane daga cikinsu kawo yanzu.

Kungiyar ta Au dai na tafiyar da akidojinta ne bisa ga turbar da tsohon shugaban ta na farko Kwameh Nkruma shekaru 50 da suka gabata ya dora ta kawo yanzu,sauyin da aka samu ba na wani abun azo a gani bane.

Kafa majalisar AU da aka akayi a yan shekarun da suka gaba ta dai abun yabawa ne,duk dacewa an gaza samarda da kundun tsarin mulki guda ko kuma babban banki dazai tafiyar da lamuran wannan nahiya.

Idan har shugabannin da gaske suke a wannan manufa tasu ta kafa hadaddiyar daular Afrika ,to ya zamanto wajibi su samar da hanyoyin warware rigingimu dake addaban nahiyar.

Ayanzu haka batutuwa da suka fi daukar hankulan kasashen duniya a wannan nahiya sune halinda alummomin zimbabwe kre ciki,da rikicin lardin Darfur da kuma Somalia a daya hannun.

Akwai kuma bukatar kasashe dake makwabtaka da juna kamar Habasha da Eritrea kana Sudan da Tschadi ,su sasanta junansu,a mai makon yake yake da suke fama dasu a yanzu haka.

Akwai manufofi da dama da kungiyarAU ta sanya a gaba dai na ganin cewa ta cimma da suka hadar da inganta tattalin arziki tare da yakar talauci da samarda ayyukanyi ,da makamantansu,nanda shekara ta 2015,kamar yadda mdd ta tsara,sai matsalar itace wannan nahiya ta Afrika na fama da matsalar karancin kudade da zata cimma wadannan manufofi nata.

Fatan kowa anan shine taron na Accra bai kasance mahawara da cacan baka kadai ba,amma a dauki matakan tabbatar dasu.