Sakamakon taron ƙoli tsakanin France da Spain | Labarai | DW | 17.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon taron ƙoli tsakanin France da Spain

An kammala taron ƙoli, tsakanin shugaban ƙasar France, Jacques Chirac, da Praministan Spain, Jose Louis Rodrigez Zapatero, taron da ka gudanar jiya, a birnin Gerone, da ke arewa maso gabacin Spain.

Jacques Chirac,yayi anfani da wannan dama ,domin gabatar da Spain, a matsayin ƙasa ta 4,a nahiyar turai,bayan France, Jamus da Italia, da ke da angizo, a fagen siyasa, da na diplomatiar a dunia.

A saboda haka,ya ƙaddamar tsari na mussamman, tare da Zapatero, da Romano Prodi na Italia,wanda ya tanadi hanyoyin warware rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Tsarin ya ƙunshi hanyoyi daban-daban, da su ka haɗa da dakatar da ɓarin wuta, tsakanin Isra´ilawa da Paletsinawa, masanyar pirsinoninn yaƙi , girka gwamnatin haɗin kan ƙasa, a Palestinu,aika tawagar mussamman daga turai a yankin, sannan a ƙarshe, a shirya taron ƙasa da ƙasa, wanda zai daddale dukkan wannan tanade-tanade.

To saidai tun ba aje ko ina ba, hukumomin Isra´ila, sun maida martani, tare da yin watsi da wannan shawarwarin.