1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon taron ƙolin AU

Yahouza S.MadobiJuly 3, 2006

Shugabanin ƙasashen Afrika su kammalla zaman taro na 16 a birnin Banjul na Gambia

https://p.dw.com/p/BtzS

Sanarwar ƙarshen wannan taro, wanda shine irin sa, na 16 da ƙungiyar Au ta gudanar, ta ƙunshi mahimman batutuwa guda 3.

Na farko dai, shugabanin sun cimma daidaito a game da tsawaita wa´a din rundunra shiga tsakani ta Afrika, a yankin Darfur,na ƙasar Sudan.

A gabanin taron, AU ta yanke shawara dakatar da wannan runduna, ranar 31 ga watan Satumber mai zuwa, a dalili da rashin issasun kayan aiki.

Bisa buƙatar Sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, wanda ya halarci taron, shugabanin sun amince da rundunar ta ci gaba da aiki, har lokacin zuwan dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia, ƙila a farkon shekara mai zuwa.

A nasa gefe Koffi Annan, ya bayana kiran wani taron masu hannu da shuni, ranar 18 ga watan da mu ke ciki, a birnin Bruxelles na ƙasar Belgium, domin roƙon su, su taimakawa AU da kuɗaɗen tafiyar da ayyuka a yankin Darfur.

Sannan a ɗaya wajen, ya alkawarta ci gaba da tantanawa da shugaban ƙasar Sudan Omar Al Beshir, da zumar ciwo kansa, ya amince da karɓar dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia a Darfur.

Batu na gaba da shugabanin su ka tanatana a kansa, ya shafi rikicin ƙasar Somalia.

Bayan kwanaki 2 na masanyar ra´ayoyi, sun yi kira ga gwamnatin riƙwan ƙwarya, da dakarun kotunan musulunci da a halin yanzu ke riƙe da manyan biranen ƙasar zuwa shawarwari.

Sannan AU, ta bada cikkaken goyan baya ga ƙungiyar ƙasashen Igad , ta yankin ƙafon Afrika, da ta ƙudurci aika tawagar dakarun shiga tsakani.

Shugaban AU, bugu da ƙari shugaban ƙasar Congo Denis Sassou Nguesso ya tabatar da cewa, ƙungiyar, zata tura dakarun haɗin gwiwa tare da Igad, domin maido doka da oda a ƙasar Somalia.

Ya ce AU ta jaddada hallacin gwamantin riƙwan ƙwarya, a Somalia, kamin yayi ga ƙasashen dunia da su yi koyi da ƙungiyar taraya Afrika, a kan wannan batu.

A game da cecekucen da ake, a kan shari´ar tsofan shugaban ƙasar Tchad Hissen Habre, shugabanin ƙasahen Afrika sun yanke hukuncin cewar kotunan Senegal za su yi masa shari´a, a maimakon ƙasar Belgium.

Saidai a game da batun tattalin arziki, wanda shine jigwan taron, babu wani abun azo a gani da aka cimma, ta la´akari da yadda batutuwan siyasa da na yaƙe yaƙe su ka mamaye mahaurori.

Sannan ta ɓangaren siyasa taron Banjul bai cimma nasara ba, ƙasashen da dama, sun ƙi amincewa da shawarwarin da komitin AU ya gabatar masu, na ɗaukar matakan hanna kwaskwarima ga kundin tsarin mulki, da nufin baiwa shugaba mai ci damar yin tazarce.