Sakamakon taro tsakanin China da Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen larabawa | Labarai | DW | 01.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon taro tsakanin China da Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen larabawa

Ƙasar China da ƙungiyar haɗin kan ƙasashen larabawa, sun cimma daidaito, a game da bunƙasa harakokin saye da sayarwa tsakanin su.

Hakan, ya biwo bayan wata tantanawa ta kwanaki 2, da ta ta haɗa wakilan China, da na ƙasashe 22, membobin Arabe Ligue, a birnin Pekin.

Ɓangarorin sun fitar da wani daftari, na daidaita harakokin kasuwanci tsakanin shekara ta 2006 zuwa 2008.

Mahimman batutuwan da daftarin ya ƙunsa, sun haɗa da ƙarfafa cinikayar makamashi, mussamman man petur da gas.

ƙasashen larabawa na sahun gaba, daga ƙasashen da ke sayar da man petur ga China.

A shekara ta 2005 saye da sayarwa tsakanin bangaroirj 2 ya kai na kuɗaɗe kimanin dalla biliyar 51.

Burin da su ke bukatar cimma, shine na lunka wannan addadi nan da shekaru 2 zuwa 3, inji sakatare Jannar na ƙungiyar haɗin kan larabawa Amr Musa.