1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SAKAMAKON HARIN BOMB A ISTAMBUL:

ZAINAB AM ABUBAKAR.November 21, 2003
https://p.dw.com/p/BvnV
Bayan harin tagwayen boma bomai daya ritsa da rayukan mutane 27 tare da raunana kusan 450 a birnin Istambul dake kasar Turkiyya,yau bankin Britania da aka kaiwa wannan hari ya fara aiki,ayayinda sauran masanaantunta ke cigaba da kasancewa cikin shirin kota kwana dangane da barazanan yan taadda.Wannan harin daya ya ritsa da karamin ofishin jakadancin Britania a wannan gari,ya auku ne kwanaki biyar bayan wasu hare hare fuda biyu daya ritsa da rayukan mutane 25 tare da raunana masu yawan gaske.
Mai magana da yawun bankin na HSBC ta bayyana cewa an bude ofisoshin hukumar dake da ress kimanin 160 da maaikata 3,500 a Turkiyyan.To sai dai har yanzu baa sanar da ko maaikatanta nawa suka rasa rayukansu a harin na jiya ba. To sai dai har yanzu kasashe da dama na cigaba da mika sakaonnin gaisuwa tare da yin Allah wadan wadannan tagwayen hare hare na Istambul.Thailand wadda yau tayi gargadi dangane da tafiye tafiye zuwa Turkiyya har sai komai ya lafa ,tayi Allah wadan wannan harin.Ofishin jakadancin kasar dake da maaikata 30 a Istambul,tayi gargadin cewa maaikatan su guji inda keda cunkosan jamaa a birnin na Istambul,kana tuni aka kammala shirye shiryen tafiyan duk wanda ke bukatan komawa gida. Shi kuwa Prime minista Thaksin Shinawatra,sake jaddada bukatar yakan ayyukan taaddanci na kasa kasa yayi a yayinda yake laantar wannan harin na jiya.
To sai dai a hannu guda kuma yansandan Turkiyya sun sanar da cafke mutane da dama a dangane da harin na jiya.Ayayinda shugaba Geoirge W Bush daya kammala ziyarar aiki na yini uku a Britania yau ya lashi takobin goyon bayansa wa Turkiyya.
Ministan harkokin wajen kasar Abdullah Gul yace an kama mutane da dama da ake zargi sai dai har yanzu babu abunda zaa iya cewa a kansu. Jaridun Turkiyyan ayau sunyi ta yayata wadannan tagwayen hare hare tare da tuni da wanda ya faru a karshen mako wanda ya kashe mutane 25 tare da raunana wasu 300 a Istambul.