Sakamakon gasar rubutun littatafai a Frankfurt
October 10, 2010Talla
Littafin wani marubuci ɗan ƙasar Isra´ila, David Grossman,ya yi nasara zama na ɗaya, daga sahun littatafen da marubuta su ka gabatar, a gasar rubuce-rubucen littatafai da ke wakana ko wace shekara a birnin Frankfurt da ke nan Jamus.
Littafin na David Grossman ya yi bayyani game da rikici tsakanin Isra´ila da Palestinu da kuma wajibcin cimma masalaha cikin ruwan sanhi.Ya fara ru´buta wannan littafi tun bayan yaƙin shekara 2006 tsakanin Isra´ila da Hizbullahi wanda a ciki ɗansa Uri ya rasa ransa.
Kamar ko wace shekara alƙalai na bayana littafin da ya hi tasiri a gasar bajen kolin littatafai ta birnin Frankfurt, tare da tukuicin Euro 25.000.
Mawalafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmed Tijani Lawal