Sakamakon binciken mutuwar John Garang | Labarai | DW | 05.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon binciken mutuwar John Garang

Komitin da aka girka, domin gudanar da bincike, a kan mussababin haɗarin jirgin saman, da ya juye, da tsofan mataimakin shugaban ƙasar Sudan, Johnn Garang, ya gabatar da sakamakon binciken da ya gudanar.

Idan dai ba a manta ba, ranar 30 ga watan juli ne, na shekara ta 2005, wani jirgin sama mai durra angulla, ya yi haɗari, wanda a sakamakon sa, John Garang tare da sauran mutane 14 su ka rasa rayuka.

Shugaban komitin binciken, ya gabatar da rahoto ga shugaban ƙasa Omar El Beshir.

A sakamakon wannan bincike,an gano cewar,, kuskure daga mutuƙin jirgin, shine ummar ibasar abkuwar wannan haɗari.

Sannan rashin cikakkar masaniya, a game inda haɗarin ya abku, ya taimaka, wajen assara rayukan da aka samu.

Wannan bincike, ya yi wastsi da zargin da ake wa, shugaban ƙasar Sudan, da kitsa maƙarƙashiya domin hallaka John Garang.