Sakamakon bayab fage a zaben Poland | Labarai | DW | 22.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon bayab fage a zaben Poland

Sakamakon bayan fage a zaben kasar Poland ya nuna cewa jamiyar adawa ita ke gaba da jamiyar firaminista Jarowslov Kaczynski inda ta lashe kashi 44 cikin dari na kuriu da aka kada.Tun farko a kanfen da yayi shugaban jamiyar adawar Donald Tusk yayi alkawarin inganta dangatakar kasar da kungiyar atraiyar turai.Kaczynski ya amince da wannan sakamako,sai dai kuma ana ganin jamiyar adawar zata nemi kafa gwamnatin hadaka ganin cewa ba zata samu kujeru da take bukata na kafa gwamnati ita kadai ba.An samu fitar masu jefa kuria mafi yawa tun bayan rushewar akidar komunisanci shekaru 20 da suka shige.An kuma kira wannan zabe ne shekaru biyu kafin lokacinda aka tsara zaa gudanar da zaben sakamkon rushewar gwamnatin hadin gwaiwa ta jamiyu uku ne a watan Agusta.