1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakacin dan Adam ya haddasa hadarin jirgin kasa na Transrapid a Jamus

September 23, 2006
https://p.dw.com/p/BuiX

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a hadarin sabon jirgin kasar mai gudun gaske dake amfani da karfin maganadisu da ake kira Transrapid, yanzu ya kai mutum 23 yayin da wasu 6 suka samu rauni. Jirgin na Transrapid ya yi karo ne da wani taragon gyaran hanyar dogo, lokacin da yake gudun kilomita 200 cikin awa daya a wata hanyar gwaji dake arewacin Jamus. Hukumomin sun ce rashin kula da wani tsarin ba da hanya ya haddasa hadarin. SGJ Angeka Merkel wadda ta kai ziyara wurin da hadaerin ya auku a jiya juma´a, ta mika ta´aziyarta ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su. Yayin da ministan sufuri Wolfgang Tiefensee ya katse ziyarar da yake kaiwa kasar Sin, inda yake tattaunawa game da fadada hanyoyin irin wannan jirgi a birnin Shanghai.