1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar Iran da Isra'ila

Abdourahamane Hassane
May 10, 2018

Gwamnatin kasar Jamus ta ce, ta damu dangane da halin da ake ciki bayan da Isra'ila ta ce sojojin Iran a Siriya sun harba rokoki akalla guda 20 kan cibiyoyin sojinsu da ke tuddan Golan.

https://p.dw.com/p/2xUn8
Syrien - Israel | Iran greift Golanhöhen an
Hoto: picture-alliance/Xinhua News Agency

Ofishin ministan harkokin waje na Jamus ya ce kai harin wata tsokana ce, kuma ya ce Isra'ila na da yancin kare kan ta. Isra'ila ta ce ta kai hare-haren na ramuwar gaya a kan cibiyoyin Iran a Siriya domin daukar fansa wanda a cikin hare-haren kungiyoyin kare haki bil Adama suka ce  an kashe mutane 23. Kasashen Faransa da Rasha  sun yi kira ga kasashen da su dakatar da ai hare-haren.