Sadiq Khan ya zama magajin garin Landan | Labarai | DW | 07.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sadiq Khan ya zama magajin garin Landan

A karon farko an zaɓi wani musulmi a matsayin magajin gari na Landan a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar adawa ta Labour.

Sadiq Khan ɗan asilin Ƙasar Pakistan mai shekaru 45 wanda maihaifinsa matuƙin babbar mota ne, ya doke dan attajirin nan Jimmy Goldesmith ɗan shekaru 41 na jam'iyyar masu ra'ayin riƙau da kashi 57 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa

Bayan bayana sakamakon zaɓen Sadiq Khan ya ce ''zaɓe ne wanda aka samu jayayya amma na yin farin ciki da zaɓin da al'ummar Landan ta yi wanda ya kasance na yaƙar tsoro ta hanyar zaɓin da ta yi da kuma samun haɗin kai saɓanin rarrabuwar kawuna jama'a.'' Sabon magajin garin na Landan zai maye gurbin Boris Johnson tsohon magajin garin dan jam'yyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta David Cameron.