Saddam ya baiyana a kotu cikin bacin rai | Labarai | DW | 13.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saddam ya baiyana a kotu cikin bacin rai

An koma shariar tsohon shugaban kasar Iraqi Saddam Hussein da mukarrabansa a yau.

Saddam din ya baiyana a kotun a fusace cike da maganganu na bacin rai yana mai fadin cewa an tilasta masa shiga kotun ne.

Saddam yaki amincewa da tayin da kotu tayin bashi sabbin lauyoyi na gwamnatin tunda lauyoyinsa sun fice daga kotun suna masu adawa da sabon alkali da aka nada a watan daya gabata..

Saddam da sauran mukarraban nasa 7 dukkaninsu sun baiyana a kotun,inda nan take shi da dan uwansa Barzan al Tikriti suka fara yin Allah wadai da kotun,suna masu fadin cewa,kotu ce da aka kafa karkashin mamayar Amurka.

A yau din wasu manyan jamian gwamnatin Saddam aka shirya zasu bada shaida,sai dai daya daga cikinsu yace an tilasta masa ne zuwa kotun,saboda haka ba shi abinda zai ce.

Alkalan kotun suna fatar cewa tsoffin jamian Saddam zasu bada da shaida da zaa samu hujjar kama Saddam da laifin kisan gilla,wadda ke dauke da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.

An dage sauraron shariar zuwa gobe talata.