1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saddam Hussein ya sake gurfana gaban kotu a Bagadaza

November 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bucy

A kuma can Iraqi a yau tsohon shugaban kasar Saddam Hussein ya sake gurfana gaban kotu a birnin Bagadaza, kwanaki biyu bayan hukuncin kisan da aka yanke masa. A wannan shari´a ta biyu tsohon shugaban da wasu mutum 6 da suka daukaka kara na fuskantar tuhuma dangane da kisan kare dangi da aka yiwa Kurdawa a shekarar 1988. Masu shigar da kara sun ce mutane kimanin dubu 180 aka halaka a hare-haren da gwamnatin Saddam ta kai a yankin Anfal. A kuma halin da ake ciki sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta yi ga kasashen Turai da ka da su yi wani sharhi akan hukuncin kisan da aka yankewa tsohon shugaban na Iraqi. Dr. Rice ta ce wannan batu ne da ya shafi ´yan Iraqi kadai. Da farko dai kasashen KTT sun yi Allah wadai da hukuncin kisan da cewa ba abin karbuwa ba ne.