1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sace maaikatan mai 6 a Nigeria

Maaikatan kamfanin mai na kasashen ketare guda shida ne aka sace a,ayayinda wani jamiin jirgin ruwa na Nigeria ya rasa ransa,alokacin da wasu yan bindiga dadi suka kaiwa wani jirgin ruwa hari yau.Kakakin rundunar sojin ruwa a Nigerai Capt. Obiora Medani,ya bayyana cewa wanda ya rasa ran nasa jamiin tsaro ne a jirgin ruwa mallakan kamfanin mai na Chevron ,wanda aka afkawa da wannan harin a jihar Bayelsa ,dake yankin kudancin kasar mai albarkatun man petur.Mr Medani yace jirgin Ruwan mai suna FPSO Oloibiri, na tsaye ne a gabar kogi domin loda masa danyan mai.Wani kakakin Nigeria dake aiki a kamfanin Chevron dake California ya bayyana cewa ,kamfanin ya rufe tasharsa dake zuba mai a jirgin sakiamakon wannan harin da aka kai yau,wanda ya rage danyan mai da ake fitarwa daga Nigeriar da ganga dubu 15 a kowace rana.