Sabuwar taswira zaman lahia tsakanin Isra´ila da Palestinu
September 11, 2007Talla
Kafofin sadarwa sun ruwaito wata sabuwar taswira zaman lahia, da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, da praminstan Isra´ial Ehud Olmert ke aiki kanta, wadda bisa dukan alamu zata cenji tsohuwar taswira zaman lahia a yankin gabas ta tsakiya.
Wannan sabuwar taswira ta ƙunshi matakai guda 8, wanda ɓangarorin2 ke kyauttata zaton na iya kawo ƙarshen balahira da ke wakana a wannan yanki.
Saidai a hukunce ya zuwa yanzu Isra´ila da Palestinu, ba su ce komai ba,a game da wannan labari.
Wannan matakai guda 8 da taswira ta kunsa sunhada da janyewra Isra´ial daga yankunanda ta mammaye na Palestinu, sannan birnin Qudus zai rabu kashi 2, ɗaya a cikin mallakar Yahudawa sannan na 2, a cikin kullar Palestinu.
A jiya litinin a gana tsakanin Mahamud Abbas da Ehud Olmert wada ita haɗuwa ta 3, daga watan Ogust da ya wuce zuwa yanzu