1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabuwar shugabar gwamnatin Jamus

A yau ne aka nada Angela Merkel sabuwar shugabar gwamnatin Jamus

Angela Merkel da Gerhard Schröder

Angela Merkel da Gerhard Schröder

Babban abin da ya fi daukar hanklain jama’a dangane kuri’ar raba gardamar dai shi ne yawan kuri’un da Angela Merkel zata samu tsakanin ‚ya’yan jam’iyyar SPD dake hadin guiwa da CDU da CSU a sabuwar gwamnatin hadin guiwar da aka nada, wacce kuma a yau in an jima ne za a yi wa wakilanta mubaya’a. Shi dai tsofon shugaban gwamnati Gerhard Schröder yayi bakin kokarinsa wajen janyo hankalin ‚ya’yan jam’iyyar ta SPD domin su ba wa Merkel cikakken goyan baya, inda ya ce shi kansa zai tsaya mata. To sai dai kuma wannan kira da yayi ba yi wani tasiri na a zo a gani ba, domin kuwa kimanin wakilan jam’iyyar 51 ne suka bijire wa Merkel a kuri’ar ta raba gardama da aka kada a asurce domin nadinta kann mukamin shugabar gwamnati. Amma duk da haka akasarin wakilan majalisar dokoki ta Bundestag sun ba ta goyan baya. A lokacin da yake ba da sanarwar nadinta kann wannan mukami, kakakin majalisar dokokin Nobert Lammert cewa yayi:

Bayan Konrad adenauer da Ludwig Erhardt da Kurt-Georg Kiesinger da Willy Brandt da Helmut Schmidt da Helmut Kohl da kuma Gerhard Schröder, ita ma Dr. Angela Merkel ta samu rinjayen da take bukata daga wakilan majalisar dokoki ta Bundestag domin zama shugabar gwamnatin Jamus ta farko a tarihin kasar.

Daidai da shuagabannin gwamnati bakwai da suka gabace ta, Angela Merkel, mai shekaru 51 da haifuwa, ta cimma nasara a zagayen farko na kuri’ar raba gardamar, inda zata shugabanci wata babbar gwamnatin hadin guiwa ta biyu da aka taba yi a nan kasar ta Jamus. Tun da farkon fari jam’iyyun hamayya da suka hada da the Greens da ‚yan gurguzu da kuma FDP suka bayyanar a fili cewar dukkan wakilansu su 166 zasu kada kuri’ar adawa ne da Angela Merkel. An saurara daga bakin Wolfgang Gerhardt kakakin jam’iyyar FDP a majalisar dokoki yana mai bayanin cewar adawar da Merkel ta fuskanta daga wakilai 51 na jam’iyyar SPD wata babbar kalubala ce ga gwamnatinta. A nasa bangaren sakatare janar na jam’iyyar SPD Hubertus Heil yayi fatali da wannan batu, inda ya ce dukkan jam’iyyun hadin guiwar sun cimma daidaituwa domin shimfida wata kyakkyawar turbar da zata saukake ayyukan gwamnatin. Ya ce ko shakka babu a game da kai ruwa ranar da aka sha famar yi domin cimma daidaituwa akan manufofin gwamnatin ta hadin guiwa, musamman ta la’akari da banbance-banbancen ra’ayin dake tsakaninsu a yake-yakensu na neman zabe, amma duk da haka wannan gwamnati ta hadin guiwa zata yi karko ta kuma kammala wa’adin mulki na shekaru hudu da aka deba mata. A halin yanzu ba abin da ya rage illa a tashi gadan-gadan a rungumi alhakin da jama’a ta dora wa gwamnatin.