1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar Kafar Labarai

January 18, 2010

Shiga neman bayanai ta yanar gizo

https://p.dw.com/p/LYgC
Hoto: LAI F

Duniya na daɗa zama tamkar wani ɗan ƙaramin ƙauye ga mutane da dama. A sassa daban-daban na duniya zaka tarar da mutane suna tuntuɓar juna ko dai ta hanyar aikewa da saƙo ta e-mail ko kafofin hulɗar jama'a ko kuma wayar salula. Shirin Ji Ka Ƙaru zai garzaya da ku wannan fage na sabuwar fasahar sadarwa.


Shin kana taɗi ta yanar gizo da abokanka a Amurka? Shin kana amfani da abin da aka kira mahaɗar sadarwa ta kyautata alaƙar jama'a? Ko shin kana amfani da yanar gizo don binciken ayyukanka na makaranta? A sassa da dama na Afirka ana fama da wahala wajen tafiyar da dukkan waɗannan abubuwa sakamakon ƙarancin hanyar sadarwa ta internet. Amma nahiyar na farfaɗowa a cikin hamzari.

Sabuwar fasahar sadarwa na taimakawa ta fuskoki da dama wajen inganta rayuwarmu – kuma musamman wayoyin salula sun taimaka aka samu sauƙin sadarwa. To sai dai kuma ita sabuwar fasahar sadarwar tana da nata matsalolin.

Wannan shi ya sanya shirin Ji Ka Ƙaru ya ga ya dace ya ba da haske a game da mamakin dake tattare da sabuwar fasahar. Wani shirin wasan kwaikwayo da aka tanada zai duba wani gungugu na 'yan kasuwa dake sha'awar shiga harkar sabuwar fasahar sadarwar. In an bi shirin sannu a hankali za a ji matsalolin da suka fuskanta lokacin da suka tsayar da shawarar buɗe shagon sadarwa na internet.