Sabuwar hukumar tabbatar da zaman lafiya a duniya ta fara aiki | Labarai | DW | 24.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar hukumar tabbatar da zaman lafiya a duniya ta fara aiki

Hukumar MDD dake kula batutuwan da suka shafi samar da zaman lafiya bayan yake yake ta fara aiki bayan wani zama na farko da ta yi don tsara aikinta. Aikin sabuwar hukumar ta tabbatar da zaman lafiya dai ya hada da taimakawa kasashe bayan sun yi fama da rikice rikice na daukar makamin. Shugaban babbar mashawartar MDD Jan Eliasson ya ce majalisar na taka muhimmiyar rawa a kokarin kawo karshen yake yake. To amma ta na fama da wahalhalu wajen tabbatar da zama lafiya mai dorewa bayan yake yake. Kamar yadda ministan harkokin wajen Denmark Per Stig Moeller wanda kasar sa ke shugabantar kwamitin sulhu a yanzu, ya nunar, da farko hukumar zata mayar da hankali akan kasashen Burundi da Liberia dake nahiyar Afirka.