1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar gwamnatin Jamus ta baiyana aniyar cigaba da neman wakilci na dauwamammiyar kujera a MDD

Sabuwar gwamnatin Jamus ta baiyana kudirin ta na cigaba da fafutukar samun dauwamammiyar kujera a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya. Ministan harkokin wajen Jamus Frank - Walter Steinmeier wanda ya kai ziyara ga sakataren majalisar dinkin duniyar Kofi Annan ya baiyana kudirin sabuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta dorawa akan matakin da tsohuwar gwamnatin ta bari ta neman wakilcin kujerar dundundun a kwamitin sulhun majalisar dinkin duniyar.

Walter Steinmeier ya kara da cewa Jamus zata cigaba da kasancewa abokiyar hulda da majalisar dinkin duniya. Yana mai cewa gwamnati mai ci na goyon bayan kudirin da kasashen G4 suka gabatar wadanda suka hada da Jamus da Brazil da India da Japan na fadada wakilcin kwamitin sulhun majalisar dinkin duniyar daga wakilai goma sha biyar zuwa ashirin da biyar. Kofi Annan da ministan harkokin wajen na Jamus Walter Steinmeier sun kuma tattauna batutuwa da suka shafi kasashen Syria da Lebanon da gudunmawar da Jamus ke bayarwa ga tabbatar da tsaro a kasar Afghanistan da kuma rawar da kungiyar tarayyar turai take takawa a gabas ta tsakiya da Kosovo.