Sabuwar gwamnatin Iraqi ta kama aiki | Labarai | DW | 21.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar gwamnatin Iraqi ta kama aiki

A yau lahadi ne sabuwar gwamnatin kasar Iraqi take fara zamanta a ofis karo na farko tun kafa ta.

A jiya asabar ne dai,mahukuntan kasar suka amince da majalisar zartarwar hadaka mai membobi 37,wanda Firaminista Nuri al Maliki ya mika musu.

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Kofi Annan da wasu shugabannin kasashen duniya sunyi maraba da kafa sabuwar gwamnatin a Iraqi bayan watanni 5 ana cacar baki akan batun nadin ministoci.

Wannan itace cikakkiyar gwamnati ta farko tun lokacinda Amurka ta mamaye kasar a 2003.

Kwana daya kuma bayan kafa gwamnatin a Iraqi an ci gaba da kai hare hare a yau lahadi,inda mutane 5 suka samu rauni a lokacinda aka jefa bam kann wata motar yan sanda a yankin Sadiyah dake kudu maso yammacin birnin Bagadaza