1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnati a Iraki

Zainab A MohammedMay 3, 2005

A karon farko cikin shekaru 50,iraki na nadin sabuwar gwamnatin democradiyya

https://p.dw.com/p/BvcB
Hoto: AP

Duk dacewa yau ne ake rantsar da gwamnatin Democradiyya akasar iraki,rikice rikice na cigaba da addaban sassa daban daban na wannan kasa.

Ayau ne ake rantsar da gwamantin Democradiyya a karo na farko cikin shekaru 50 da suka gabata a kasar ta iraki,sai dai har yanzu babu tabbas dangane da batun zaman lafiya a wannan kasa tun bayan mamayan da Amurka tayiwa jagoranci a watan maris din shekara ta 2003.

Gabannin wannan buki na rantsar da sabuwar gwamnatin dai ana cigaba da samun tashe tashen hankula tare da kai hare haren boma bomai a sassan kasar.A yau ne wasu yan bindiga dadi suka harbe wani babban jamiin gwamnatin kasar,ayayinda wasu yansanda uku suka gamu da ajalinsu a wani harin daya ritsa dasu a arewacin birn Bagadaza.

Major Naef Hamid ya bayyana cewa a hare hare daban daban guda uku a garin Samarra dake da yawan yan darikar Sunni ,mai tazarar km 125 arewacin bagadaza,jamian yansanda guda uku ne suka rasa rayukansu a yau.Atsakiyar birnin na Bagadaza kuwa bomb ya fashe a wata mota kusa wurin da jamian yansanda ke sintiri a gunduwar gazaliya,inda harin ya raunana jamiin yansanda guda da wani farar hula,ayayinda wasu boma bomai guda uku suka tarwatse a wata unguwa dake fadar kasar ,wanda shima ya raunana yansanda uku.

Rahotanni daga garin Ramadi mai tazarar km 110 yammacin Bagadaza na nuni dacewa akalla fararen hula 14 suka rasa rayukansu ayayin wata arangama tsakanin sojin Amurka da jamian tsaron Iraki day an yakin sari ka noke a daya hannun.

Directan Asibitin Ramadi Moneim Aaaftan yace fadan ya barke ne a wajen da yansanda ke bincike akan hanyar ficewa daga wannan gari,inda yace akasarin wadanda suka rasa rayukan nasu fararen hula ne maaikata.

Tun bayan sanar4 da sabuwar gwamnatin farar hula ranar alhamis data gabata,ake cigaba da samun karuwan hare haren boma bomai a sassa daban daban na wannan kasa.gabannin wannan buki na rantsar da sabuwar gwamnatin Democradiyyan dai,jamian tsaro sun dauki tsauraran matakan tsaro na tabbatar da kariya tare da nasaran gudanar da wannan buki ba tare da wata matsala ba.

Wannan buki wanda ke gudana a yankin dake dauke da manya jamian gwamnatin Iraki wanda aka fi sani da sunan Green zone,na mai kasancewa gwamnatin democradiyyan farko a wannan kasa,inda Premi minister Ibrahim Jaafari ke karbar ragamar gwamnati da gwamnatin rikon kwarya da Amurka ta nada a karkashin jagorancin iyad Allawi.

Sabuwar gwamnatin dai na rataye da hakkin samarwa Iraki zaunanniyar kundun tsarin mulki,tare da gudanar da sabon zabe nan da karshen wannan shekara da muke ciki.