Sabuwar dokar zaman baki a Jamus | Siyasa | DW | 25.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabuwar dokar zaman baki a Jamus

A wani mataki na bai wa bakin da basu da takardun zama wata dama ta zama na dindindin Jamus ta cimma wata daidatuwa akan wata sabuwar doka bisa manufa

Ita wannan maganar dai, musamman, ta shafi wasu baki ne su kimanin dubu 180, wadanda suka yi shekara da shekaru ana hakuri ne da zamansu a nan Jamus, amma ba tare da cikakkun takardun zama ko kama aiki a kasar ba, kuma ana iya korarsu a duk lokacin da zarafi ya kama. Bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi, a makonnin baya-bayan nan an cimma daidaituwa tsakanin jami’iyyun gwamnatin hadin guiwa, wadda za a yi zaman farko kanta a majalisar dokoki ta Bundestag a yau alhamis. Wannan daidaituwar ta shafi wani adadi ne na bakin da za a basu wata dama ta ci gaba da zama na dindindin a Jamus. Hakan kuwa ya zo daidai da tsarin dokokin kungiyar tarayyar Turai dangane da zaman baki a kasashen kungiyar. Ministan cikin gida na Jamus Wolfgang Schäuble ya ce daidaituwar da aka cimma tana ba da cikakken la’akari da dokar kaka-gida da kuma canje-canjen da aka samu ta fuskar tsaro sakamakon barazanar harin nan na bom da ya ci tura a kasar shekarar da ta wuce. Schäuble ya kara da cewar:

“Wannan daidaituwa gaba daya zai taimaka a samu kara kyautata zaman cude-ni-in-cude-ka tsakanin Jamusawa da takwarorinsu baki da suka dade da zama a wannan kasa.”

To sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin ‘yan gudun hijira sun bayyana takaicinsu da wannan daidaituwar da aka cimma bayan kai ruwa ranar da aka shafe lokaci mai tsawo ana yi. Kuma kawo yanzun ba wanda ya san ko mutum nawa ne daga cikin mutane dubu 180 zasu samu wannan alfarma. Masu sukan lamirin sabuwar dokar na haufin cewar mai yiwuwa wasu ‘yan kalilan ne zasu ci gajiyar lamarin sannan ragowar kuma su ci gaba da kasancewa cikin hali na rashin sanin tabbas a game da makomarsu a nan Jamus. Domin kuwa duk wani mai so ya samu wannan alfarma tilas ne ya cika wasu jerin sharudda. Misali mutumin da ba ya da aure tilas ne ya kasance yayi zama na tsawon shekaru takwas a Jamus, a yayinda ma’aurata kuma aka shardanta musu zama na shekaru shida. Bugu da kari kuma alfarmar ba ta shafi wanda ya ba da shaidar zul domin neman mafakar siyasa a Jamus ba. Kazalika da wanda aka taba samunsa da mugun laifi. Ita ma kwarewa a harshen Jamusanci na daga cikin sharuddan da aka shimfida hade da wata tabbatacciyar shaidar dake nuna cewar mutum na da aikin yi. Wani abin da masu korafi ke tofin Allah tsine akansa dangane da sabuwar dokar shi ne shardanta kwarewa a harshen Jamusanci ga duk matar dake sha’awar da riski mijinta a nan Jamus. Amma wannan sharadin bai shafi baki daga Amurka da Kanada da Japan ko Koriya ta Kudu ba, wai saboda babu wata wahalar zama na cude-ni-in-cude-ka da su.