1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabuwar dokar zama dan kasa a Baden-Württenberg

Jihar Baden-Württenberg ta kudancin Jamus ta gabatar da sabuwar dokar zama dan kasa a wannan jiha

Magoya-bayan sabuwar dokar, wacce ainifi ta fi shafar musulmi, musamman wadanda suka fito daga kasashen kungiyar Musulmi ta Duniya OIC, sun bayyana cewar wannan doka tana da nufin ba da cikakkiyar kariya ga al’umar kasar daga masu akidar tsananin kishin addini, lamarin da Turkawa ‚yan ci rani suka bayyana adawarsu da shi. Tun dai abin da ya kama daga daya ga watan janairu bayyana mubaya’a ga dukkan manufofin Jamus da girmama tsarin mulki da kuma dokokin kasar ba zasu wadatar ga Musulmin dake neman zama ‚yan kasa a jihar Baden-Württenberg dake kudancin kasar ba. A wannan jiha tun daga yanzu duk wani Musulmin dake neman zama dan kasa, musamman ma ‚yan usulin Turkiyya da Albaniya, sai ya fuskanci tambayoyi a game da ra’ayinsa dangane da ‚yan daudu da ire-iren kawancen nan tsakanin ‚yan mata da samari gabanin aure da kuma matakan shan fansa da ragowarsu. Wato dai manufar wadannan tambayoyin shi ne ko masu neman zama ‚yan kasar Jamus din a shirye suke su yi biyayya ga tsarin dokokin kasar a maimakon shari’ar Musulunci. A lokacin da yake bayani wani jami’in ma’aikatar cikin gida ta jihar Baden-Württenberg mai suna Reiner Grell ya ce dalilin gabatar da wannan doka shi ne binciken ra’ayin Musulmi ‚yan ci-rani da aka gudanar. Sai ya kara da cewar:

Musabbabin haka shi ne sakamakon wani nazarin da aka yi, inda kashi 21% na Musulmin dake zaune a nan Jamus suka bayyana ra’ayin cewar akwai sabani tsakanin tsarin dokokin Jamus da shari’ar Musulunci.

Grell ya kara da cewar wani muhimmin abin da muke so mu ba da la’akari da shi shi ne ganin cewar iyayen yara sun girmama bukatun ‚ya’yansu manya. Ba zamu yarda iyayen yara su rika nuna karfin iko suna gallaza wa ‚ya’yansu ko tilasta su auren dole ba.

Tambayoyin dai a baya ga maganar addini, kazalika sun hada da ra’ayin mutum a game da akidar nan ta tsananin kishin addini ko ta’addanci. To sai dai kuma kamar yadda muka yi bayani tun farko maganar ta shafi Musulmi ne daga kasashen kungiyar Musulmi ta duniya su 57. A sakamakon haka shugaban majalisar tarayya mai kula da al’amuran baki Mehmet Kilic yake batu a game da wata manufa ta wariya. Mehmet ya ci gaba da bayaninsa da cewar:

Wadannan tambayoyin ba zasu tsinana kome ba wajen bin diddigin ‚yan ta’adda, saboda tun da farkon fari sun san irin amsar da zasu bayar. Ainifin wadanda abin zai shafa sune ‚yan ba ruwanmu, wadanda suka yi shekara da shekaru suna tafiyar da al’amuran rayuwarsu a Jamus tare da girmama dokokin kasar. A nan ne take kasa tana dabo.

Tuni dai kungiyoyin musulmi da na Turkawa suka ce zasu yi adawa mai tsanani ga dokar kuma zasu gabtar da kara gaban kungiyar tsaro da hadin kai a nahiyar Turai OSCE domin ganin jihar Baden-Württenberg ta dakatar da wannan mummunar manufa ta wariya wajen ba da izinin zama dan kasa ga musulmi a Jamus.