Sabuwar dokar zaɓe a Palestinu | Labarai | DW | 15.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar dokar zaɓe a Palestinu

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas ya sa hannu akan wata sabuwar dokar zabe.

A cewar dokar ya zama wajibi nan gaba wanda zai ajje takara a zaɓɓuɓuka daba-daban, ya yi amana da dokokin ƙungiyar PLO, sannan ya mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma baya, tsakanin Isra´ila, da Palesitinu a yunƙurin warware rikicin da ke tsakanin su.

Paƙat !! wannan mataki ya maiyar da Hamas saniyar ware a harakokin zaɓen Palestinu.

Ba da wata wata ba, shugabanin Hamas su ka watsi da wannan doka wadda su ka ce ,ta saɓawa demokraɗiya.

Tun bayanda kungiyar Hamas ta kwace zirin Gaza shugaba Mahamud Abbas ke ɗaukar dokoki makamantan wannan, wanda ba cilas ba, sai sun bi ta hanyar Majalisar Dokoki,inda Hamas ke da rinjaye a cikin ta.

A wani taron manema labarai da yayi ,Mahamud Abbas ya buƙaci ƙungiyar Hamas ta gane kuren ta, ta kuma bada kai bori ya hau, ta hanyar anfani da umurnin gwamnatin sa.

A watan juli da ya gabta, majalisar ƙoli ta ƙungiyar PLO, ta yi kira ga Mahamud Abbas, ya shirya saban zaɓen yan majalisun dokoki a Palestinu.