Sabuwar dokar ′yan gudun hijira ta Trump ta gamu da cikas | Labarai | DW | 11.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar dokar 'yan gudun hijira ta Trump ta gamu da cikas

Dokar da shugaban Amirka Donald Trump ya sake sakawa hannu kan siyasarsa ta 'yan gudun hijira, ta soma gamuwa da cikas daga mashara'antun kasar.

USA Trump signiert Durchführungsbeschluss zum Einreiseverbot (Reuters/C. Barria)

Shugaban Amirka Donal Trump na saka hannu kan dokar 'yan gudun hijira

Tuni dai wani alkali ya yi wasti da batun hana matar wani dan kasar Siriya tare da diyarta shiga kasar ta Amirka, ganin cewa tuni mijinta yake a matsayin dan gudun hijira a kasar ta Amirka. Wanda ya shigar da karan dai wani Musulmi ne dan kasar Siriya, wanda ya gujewa yake-yaken kasar ta shi tun daga shekara ta 2014, sannan kuma ya shigar da takardar neman mafaka ga matarsa da kuma diyarsu da su suka kasance a birnin Aleppo, kaman yadda aka gabatar da wadan nan bayannai a gaban kotu.

Alkali William Conley na jihar Wisconsin da ya duba batu, ya ba da izinin dakatar da wannan doka ta wani dan lokaci kafin su yi nazarinta ga baki daya, sannan kuma ya ce, wanda ya shigar da karan ya gabatar da kwararan shaidu da ka iya samun sa'ar gamsar da kotu.