Sabuwar dokar ta bace a ƙasar Nepal | Labarai | DW | 23.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar dokar ta bace a ƙasar Nepal

A ƙasar Nepal, hukumomin sun ƙara kafa dokar ta bace, a sahiyar yau lahadi, bayan gagaramar zanga zangar da ta haɗa dubbunan ɗaruruwan mutane, a Katmandu babban birnin ƙasar,ranar asabar ɗin jiya.

Wannan sabuwar doka, na hanna fita daga ƙarfe 11 na rana, zuwa 8 na dare.

Yau sati 2 kenan da su ka gabata, haɗin gwiwar jam´iyun adawa su ka fara zanga zangar baji ba gani,da nuffin kiffar da Sarki Gyanendra, da ya ɗare karagar mulkin ƙasar, bayan ya russa da gwamnati, a shekara da ta gabata.

A sakamakon matsin lambar, da ya ke fuskanta, cikin yan kwanakin nan, mai martaba sarki, ya yi matukar nadama, ya kuma yi alkawarin shirya zaɓuka kamar yada jam´iyun na adawa ke bukata, sannan ya gayyace su,su bashi sunan mutum guda, daga cikin su, wanda zai naɗa Praminsita.

Jam´iyun adawa, sun sa ƙafa sun shure wannan tayi.

Sun nace a kan matsayin su, na sai sarki Gyanendra, yayi murabus.

Kazalika, sun sha alwashin ci gaba da zanga zanga, har sai sun cimma wannan buri.

Daga farkon rikicin, zuwa yanzu, mutane 12 su ka rasa rayuka, sannan da dama su ka ji mummunan raunuka.