1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar Dokar Kaka-Gida Ta Jamus

May 26, 2004

Dukkan jam'iyyun siyasar Jamus sun bayyana gamsuwarsu da daidaituwar da suka cimma akan sabon kundin dokar kaka-gida a kasar

https://p.dw.com/p/BvjI
Shugaban gwamnati Gerhard schröder da ministan cikin gida Otto Schily lokacin taron manema labarai bayan cimma daidaituwa akan kundin dokar kaka-gida
Shugaban gwamnati Gerhard schröder da ministan cikin gida Otto Schily lokacin taron manema labarai bayan cimma daidaituwa akan kundin dokar kaka-gidaHoto: AP

Masu iya magana kan ce wai na-gari-na-kowa mugu kuma sai mai shi. Kwana daya bayan daidaituwar da aka cimma a sabanin da ake yi akan sabuwar dokar kaka-gida a nan Jamus, kowace daga cikin jam’iyyun siyasar kasar na buga kirji da irin gudummawar da ta bayar domin cimma wannan manufa. Wato dai kowace daga cikinsu na ikirari ne cewar ta cimma biyan bukatunta, ko da yake akalla ministan cikin gida Otto Schily ya yaba da rawar da sauran jam’iyyun siyasar na Jamus suka taka bisa manufa. Ya ce dukkan jam’iyyun CDU da CSU da The Greens sun taka rawar gani domin cimma wata manufa bai daya dangane da wannan muhimmin kundi na garambawul. Wannan ci gaba ne da zai yi kyakkyawan tasiri ga jama’a. To sai dai kuma ministan ya kara da gabatar da gargadi ga ‚yan Christian Union a game da wani yunkuri na yin daidai da manufofin da aka cimma daidaituwa kansu a dunkule. A yanzun bakin alkalami ya bushe, babu wata magana da sake bitar kundin. Wasu daga cikin shuagabannin Christian Union sun kalubalanci matsayin da jam’iyyar Greens ta dauka a game da rarrabewa tsakanin maganar kaka-gida da ta tsaron lafiyar jama’a a cikin gida. Wajibi ne a dauki nagartattun matakai na mayar da mutanen da ake tuhumarsu da kasancewa ‚ya’yan wata kungiya ta ‚yan ta’adda ko ‚yan fataucin mata da bakin haure, zuwa kasashensu a cikin gaggawa. Wakilin jam’iyyar The Greens akan manufofin tsaron lafiyar jama’a a cikin gida Volker Beck ya ce ainihin abin dake ci wa jam’iyyarsa tuwo a kwarya a game da dokar ta kaka-gida shi ne na neman bayanai akan duk mutumin dake sha’awar karbar takardun fasfo na Jamus nan gaba saboda a tantancen tarihinsa ko Ya-Allah mai zazzafar akida ce ta siyasa. Sai dai kuma a daya bangaren ya yaba da ci gaban da aka samu game da ba wa matan dake fuskantar muzantawa a kasashensu wata dama ta samun mafaka a nan kasar. Amma abin takaici shi ne kasancewar an yi tuya ne aka manta da albasa, domin kuwa dokar ba ta ba da la’akari da bukatar kwararrun masana ‚yan kaka-gida da ake yi domin cike gibin da Jamus ke fama da shi a wannan bangare dake da muhimmanci ga makomar tattalin arzikinta ba. Duk dai da haka, akalla dokar tana ba da kwarin guiwa, in ji shugaban majalisar ciniki da masana’antu ta Jamus Ludwig Georg Braun. Za a samu sabbin guraben aikin yi ga jama’a dangane da dimbim kwararrun masana baki da suka tsayar da shawarar ci gaba da zama a nan kasar ta Jamus.