Sabuwar Dokar Ayyukan Deutsche Welle | Siyasa | DW | 18.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabuwar Dokar Ayyukan Deutsche Welle

Dukkan jam'iyyun siyasar Jamus dake da wakilci a majalisar dokoki ta Bundestag sun goyi bayan sabunta manufofin ayyukan tashar Deutsche Welle lokacin wani zaman mahawara da suka yi a yammacin jiya alhamis

Daya daga cikin wasikun masu sauraro dake yaba wa ayyukan Deutsche Welle

Daya daga cikin wasikun masu sauraro dake yaba wa ayyukan Deutsche Welle

Kusan dukkan wakilan majalisar dokokin ta Bundestag sun hakikance da muhimmancin karfafa matsayin tashar Deutsche Welle (DW), a sakamakon haka suka amince da kasafta mata isasshen kudi ta yadda zata samu kafar gudanar da ayyukanta na rediyo da telebijin da kuma hanyar sadarwa ta yanar gizo, wato Internet, salin alin ba tare da matsala ba. An ji wannan bayanin daga bakin ministar al’adu da yada labarai ta Jamus Christina Weiss, wadda ta kara da cewar dukkan wakilan jam’iyyun siyasar kasar sun hakikance da muhimmancin sabunta tashar DW ta yadda zata iya daukar nauyin da aka dora mata na wayar da kan mutane a game da al’amuran Jamus a kasashen ketare, a fannoni na siyasa da al’adu da tattalin arziki da kuma zamantakewar jama’a. ‚Yan hamayya na Christian Union, ko da yake sun yi marhabin da shawarar da gwamnati ta bayar, amma sun ce wajibi ne a ba wa tashar cikakken ikon aiwatar da kudaden da gwamnati ta kasafta mata akan hanyoyin da take ganin sun fi dacewa. A lokacin da yake bayani wakilin CDU Bernd Neumann cewa yayi:

Irin wannan tsari da ake bukatar gani daga DW abu ne na dogon lokaci, kuma ba zata yiwu a tafiyar da al’amuran gidan rediyo tamkar wata hukuma dake magana da yawun gwamnati ba. Muhimmin abun da ake bukata a game da aikin rediyo shi ne tsare-tsare na dogon lokaci ta yadda gidan rediyon zai samu sukunin tafiyar da ayyukansa ba tare da tangarda ba.

Kusan dai dukkan masu magana da yawun sauran jam’iyyun siyasar dake da wakilci a majalisar dokokin ta Bundestag sun bayyana bukatar dake akwai wajen cike wannan gibi a shawarar da gwamnati ta gabatar. ‚Yan hamayya zasu gabatar da tasu shawarar game da wannan batu. An saurara daga bakin Hans-Joachim Otto, wakilin FDP yana mai bayanin cewar:

A yayinda a bangare guda aka rika bunkasa yawan kasafin kudin tashoshin rediyo da telebijin na Jamus ARD da ZDF, ita DW kakaba mata takunkumin tsumulmular kudi aka yi a shekarun baya-bayan nan. A saboda haka ya zama wajibi a samu hadin kai a tsakanin illahirin jam’iyyun siyasar kasar nan akan wani takaimaiman kudurin da zai taimaka a dora ayyukan tashar DW kan wata hanya madaidaiciya. Muhimmin abu shi ne a cimma daidaituwa akan wata manufa mai sassauci domin karfafa matsayin wannan tasha domin jure nauyin da aka aza mata.

A cikin makonni da kuma watanni masu zuwa ne kwamitocin rikon kwarya da aka nada zasu yi bitar sabon daftarin tsarin ayyukan tashar ta DW domin wanzar da shi nan da karshen shekara.